Gwamnatin Jihar Filato ta bayar da umarni ga maniyyatn jihar 400 da suka biya kudadensu a shekarar 2014, amma ba su samu tafiya aikin Hajjin ba, su zo su cika kudaden kujerarsu idan suna bukatar tafiya aikin hajjin bana.
Kwamishinan kananan Hukumomi da Masarautu kuma Amirul Hajjin Bana na Jihar, Alhaji Yusuf dayyabu Garga ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da ’yan jarida kan shirye-shiryen aikin Hajjin bana a jihar.
Kwamishinan ya ce gaskiyar magana ita ce a shekarar 2014 akwai maniyyatn jihar da suka biya kudadensu, amma ba su samu tafiya aikin Hajjin ba. Kuma da wannan gwamnati ta zo ta yi bincike kan maganar ta gano cewa an karbi kudadensu an ba su rasidai amma babu kudaden a asusun gwamnatin jihar. “Zuwa yanzu hukumomin EFCC da ICPC suna bincike kan wannan lamari. Don haka gwamnatin jihar ta tausaya wa wadannan maniyyata ta ba da umarnin duk maniyyacin da yake da ikon cika sauran kudin to ya cika, idan kuma mutum ba ya da ikon cikawa za a ba shi kudin da ya bayar tun farko,” inji shi.
Alhaji Yusuf dayyabu Garga ya ce sakamakon wannan dama da aka ba maniyyatan da dama sun cika kudin kuma za su tafi aikin Hajjin bana, wadansu kadan ne ba su cika ba, kuma za su jira da zarar an tafi aikin Hajji da kwana biyar, za a ba su kudadensu da suka biya tun farko.
Ya ce a bana an bai wa Jihar Filato kujera 1,400 amma maniyyata 1,128 ne aka tabbatar za su tafi aikin Hajji daga jihar, kuma ana sa ran za su fara tashi ne a ranar Litinin mai zuwa.
“A bana maniyyatan Jihar Filato za su tashi ne daga Jihar Bauchi ba Kaduna da aka saba tashi a kowace shekara ba.Kuma ina kira ga maniyyatan jihar idan sun isa kasa Mai tsarki, su tabbatar sun yi wa kasar nan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’o’in alheri. da suka biya kudin kujera a shekarar 2014 za su sauke farali a bana