✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maniyyatan da aka yi wa rigakafin COVID-19 ne kadai za a bari su shiga Saudiyya

Matakin, a cewar Saudiyya, zai sa Masallatan Harami su debi mutane masu yawa lokacin azumi.

Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da cewa maniyyatan da aka yi wa rigakafin COVID-19 ne kadai za su samu izinin shiga kasar domin ibadar Umrah a Watan Azumi mai kamawa.

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah ta kasar a cikin wata sanarwa ranar Litinin ta ce za ta yi la’akari da rukuni uku ne na mutanen da aka yi wa rigakafin.

Mutanen, a cewarta sun hada da wadanda aka yi wa rigakafin sau biyu, wadanda aka yi wa sau daya cikin kwanaki 14 kafin lokacin tafiyarsu da kuma wadanda suka warke daga cutar —su ne kawai za a bari su yi ibada a biranen kasar masu tsarki.

Matakin, a cewar gwamnatin zai sa Masallatan Harami na Makkah da Madina su debi mutane masu yawa lokacin azumi.

Saudiyya dai ta ce dokar za ta fara aiki ne daga farkon watan Ramadan wanda ake sa ran zai fara a cikin mako mai zuwa.

Sai dai sanarwar ba ta fadi tsawon lokacin da matakin zai dauka ana amfani da shi ba, ko kuma zai shafi maniyyata aikin Hajji ko a’a.

A watan Yulin 2021 dai kasar ta kyale alhazan kimanin 10,000 suka yi aikin Hajjin, sabanin kimanin mutum miliyan biyu da rabi da suka yi ibadar a 2019.