✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maniyyatan bana su cika kudin kujerarsu kafin ranar Litinin — Hukumar Alhazai

Ya zuwa yanzu an sayar da kujerun kusan guda dubu biyu daga cikin dubu shida.

Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano ta nemi maniyyata aikin Hajji bana da su yi kokarin cika kudin kujerarsu kafin nan da ranar Litinin, 12 ga watan Fabarairu.

Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Laninu Danbappa ne ya bayyana haka a lokacin bikin bude shirin farko na bita na Aikin Hajjin bana wanda aka yi a Kano.

Danbappa ya bayyana cewa a bara Hukumar Aikin Hajji ta Kasar Saudiyyta ta dauki matakin gudanar da ayyukan da suka shafi Aikin Hajji a kan lokaci ba kamar yadda aka saba gudanarwa a baya ba.

“Muna kira ga maniyyata musamman masu adashin gata da su yi gaggawar cika kudinsu ta kai Naira miliyan hudu da dubu dari bakwai kafin nan da ranar 12 ga Fabarairu.

“Haka su ma wadanda ba su kawo fasfo dinsu ba da su yi gaggawar yin hakan domin nema musu biza kasancewar Kasar Saudiyya za ta rufe bayar da buza a ranar 29 ga watan Afrilu.”

Ya kuma kara da cewa za a gudanar da bitar ne a matakai domin bai wa maniyyata damar samun fadakarwa kan Aikin Hajji da kuma sabbin tsare-tsare da mahukuntan Saudiyya da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON suka bullo da su a bana.

Hukumar ta bayyana cewa tuni aka hada malaman addinin Musulunci domin gudanar da bitar a shiyyoyi 13 da ke fadin jihar.

Da yake karin haske game da yawan kujerun da hukumar ta sayar a yanzu, Darakta Janar din ya ce zuwa yanzu an sayar da kujerun kusan guda dubu biyu daga cikin dubu shida da Hukumar da ke kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ware wa maniyyatan Kano.

Wakilin Sarkin Kano a taron Dan Anar din Kano, Alhaji Aliyu Harazimi ya shawarci.maniyyata da su shiga duk shirye-shiryen da hukumar ta shirya da nufin taimaka musu wajen samun aikin hajji mai karbuwa.

Ya shawarci maniyyata, musamman wadanda wannan zai kasance aikin Hajjinsu na farko, da su yi amfani da wannan bitar da kuma inganta iliminsu na Musulunci kan ayyukan Hajji.