✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester United za ta sayar da Juan Mata

Kocin Manchester United da ke Ingila Louis ban Gaal ya baytyana cewa a watan Janairun shekara mai zuwa ne yaka sa ran sayar da dan…

Kocin Manchester United da ke Ingila Louis ban Gaal ya baytyana cewa a watan Janairun shekara mai zuwa ne yaka sa ran sayar da dan kwallonsa Juan Mata don ganin ya samu gurbin maye shi da dan kwallon taskiyar Hollan wanda yanzu haka yake wasa a kulob din Roma na Italiya Kebin Stootman
ban Gaal ya nuna rashin gamsuwa da yadda Juan Mata yadda yake buga kwallo  a kakar wasa ta bana musamman a wasan da Manchester United ta yi da na kPR a gasar rukunin Premier na Ingila inda United ta samu nasara da ci 4-0.  Duk da cewa Juan Mata yana daga cikin wadanda suka zura kwallo a ragar kPR a ranar kuma ita ce kwallonsa ta takwas daga cikin wasanni 10 da ya yi hankalin kocin bai kwanta a kan dan kwallon ba.
Dalilin haka ne ma kocin ya ki sanya Mata a farkon wasan da United ta yi rashin nasara da ci 5-3 da kulob din Leicester City a ranar Lahadin da ta wuce.  Daga baya ne ya sako shi bayan dawowa hutun rabin lokaci, amma duk da haka kocin bai gamsu da yadda dan kwallon ya yi wasa ba.