Ga dukkan alamu kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fita daga jerin kungiyoyin kwallon kafa guda uku mafi arziki a duniya.
Kulab din Real Madrid da na FC Barcelona da kuma na Bayern Munich ne a sahun farko da na biyu da na uku (bi-da-bi) a jerin sunayen da kwararru suka fitar bayan sun yi amafani da kudin shigar da kungiyoyin kwallon kafar suka samu a kakar wasanni ta shekarar 2012 zuwa shekarar 2013.Manchester United ce ta hudu a jerin kungiyoyin kwallon kafar.
Kafar sadarwa mai zaman kanta da ke bibiyar kudin shigar kungiyoyin kwallon kafar mai suna Sport News ce ta bayyana haka a ranar Talata da ta wuce.
Ta bayyana kulob din Real Madrid ya samu jimillar Yuro miliyan 518 da digo tara a matsayin kudin shiga da hakan ya sa ta wuce kulob din Manchester United da yake da tarihin kasancewa kulob din da ya fi arziki a duniya a shekarun baya.
Haka kuma kulob din da ke buga wasa a Faransa mai suna Paris Saint Germain (PSG) ne ya kasance na biyar a jerin kungiyoyin kwallon kafar da suka fi kudi a halin yanzu.
Sai dai duk da fadowar da kulob din Man U ya yi, kudin shigarsa ya karu daga yuro miliyan 395 da digo tara zuwa yuro miliyan 423 da digo takwas.
Haka kuma kudin shigar da Kulob din Bayern Munich da ke Jamus ya samu ya karu da yuro 62 da digo takwas kwatankwancin kashi 17 cikin dari ne zuwa yuro 431 da digo biyu da hakan ta sa ya koma matsayi na uku a jerin kungiyoyin kwallon kafar da suka fi samun kudin shiga a ha9lin yanzu.. Shi kuwa kulob din Turkiyya mai suna Galatasaray da kuma na Fenerbahce sun kasance na 19 da kuma na 20 ne a jerin sunayen.
Kodayake kulob din Liberpool na Ingila ya samu karin kudin shiga da kashi tara cikin 100 amma duk da haka ya fita daga jerin kulab 10 da suka fi arziki a karon farko tun cikin shekarar 1999.
Manchester United ta fita daga sahun kulob uku da suka fi kudi a duniya
Ga dukkan alamu kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fita daga jerin kungiyoyin kwallon kafa guda uku mafi arziki a duniya.Kulab din Real Madrid…
