Kungiyar Manchester City ta rage wa Liverpool saukin lashe gasar Premier bayan da ta lallasa Arsenal da ci 3-0 a filin wasa na Etihad ranar Laraba.
Dan wasan gaba na kungiyar ta City Raheem Sterling ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal kafin bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida da kungiyar City din ta samu bayan dan wasan baya na Arsenal, David Luiz, ya samu jan kati.
- Ganduje ya bude gidajen kallon kwallo
- Dalilan da ke hana ’yan Arewa haskawa a kwallon kafar Najeriya
‘Yan wasan tsakiya na City, Kevin De Bruyne da Phil Foden, suka jefa kwallo ta daya da ta biyu da suka tabbatar wa kungiyar tasu nasararta ta farko bayan dawowa gasar Premier.
Da Manchester City ta gaza samun nasara, Liverpool tana da damar lashe gasar idan ta lallasa Everton ranar Lahadi.
A halin yanzu dai kungiyar ta Liverpool za ta bukaci samun nasarori biyu kafin ta dauki kofin gasar wanda ba ta lashe ba a shekaru 30 da suka gabata.