Manchester City ta lashe kofin gasar Firimiyar Ingila ta bana bayan ta farke kwallo biyu da Aston Villa ta zira mata a filin wasa na Etihad.
Wannan shi ne dai karo na shida ke nan da kungiyar ta lashe gasar a tarihi.
- EFCC ta saki tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilai Patricia Etteh
- IPOB: ’Yan bindiga sun fille kan dan majalisa a Anambra
Kungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta ta kare kakar ta bana da tazarar maki daya kacal tsakaninta da Liverpool, wadda ta doke Wloves 3-1 a wasan karshen da aka fafata a Yammacin Lahadi.
Kwallo biyu da Ikay Gundogan ya ci da kuma wadda Rodri ya zira a cikin minti shida kacal su ne suka bai wa City nasara inda ta lashe wasan da 3-2.
Villa ta shiga gaba a wasan tun farko ta hannun Matty Cash da Philippe Coutinho.