✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester City ta doke United a wasan karshe na Kofin FA

Manchester City ta dauko hanyar lashe dukkan kofunan da ta haska a kakar wasa ta bana.

Manchester City ta dauki Kofin FA bayan ta doke Mancheter United da ci 2-1 a wasan da suka yi ranar Asabar.

Ilkay Gundogan ne ya zura dukkan kwallayen biyu, lamarin da ya sa Manchester City ta lashe kofi na biyu a kakar wasan bana ya zuwa yanzu.

Tuni dai City ta dauki Kofin Gasar Firimiya, don haka yanzu abin da ya rage mata shi ne Kofin Zakarun Turai inda za ta fafata da Inter Milan a makon gobe a Istanbul don nemansa.

Idan ta lashe shi za ta bi sahun United, wadda a shekarar 1999 ta lashe kofuna uku.