✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Man United za ta gina sabon filin da zai ɗauki ‘yan kallo 100,000

An mayar da hankali kan wani sabon gini maimakon gyara filin wasan da ake da shi.

Mamallakan Manchester United na fatan yanke shawara ta karshe kan ko za su kashe sama da fam biliyan biyu, domin gina sabon filin da zai ɗauki ’yan kallo 100,000 nan da karshen shekarar 2024.

Wanda ya mallaki hannun jari mafi tsoka a ƙungiyar, Sa Jim Ratcliffe yana son a gina katafaren fili, kuma tuni aka kafa kwamiti tare da majalissar Trafford, don tantance yiwuwar gina sabon filin wasa da sake fasalin Old Trafford.

Lord Sebastian Coe ne ke jagorantar shirin, kuma ya haɗa da babban magajin garin Manchester, Andy Burnham da tsohon kyaftin din Red Devils, Gary Neville.

Wata majiya ta ce tuni sun tattauna har sau huɗu, inda suka mayar da hankali kan wani sabon gini maimakon gyara filin wasan da ake da shi, wanda zai ci kusan £1.2bn kuma zai dauki tsawon lokaci kafin a kammala shi.

An jaddada cewa ba a yanke hukunci ba.

Yarjejeniyar Ratcliffe ta fan biliyan 1.25 ta hannun jarinsa na kashi 27.7% a kungiyar ta hada da fam miliyan 237 don saka hannun jari a filin wasa na kungiyar nan gaba.

Ƙamfaninsa na Ineos ya karɓi ayyukan ƙwallon ƙafa daga yawancin masu ƙungiyar, wato iyalan Glazer.

Matsalolin da aka samu wajen sabunta Old Trafford mai daukar ’yan kallo 74,310, wanda ya kasance filin Manchester United tun 1910, ya hada da layin dogo a bayan benen Sir Bobby Charlton Stand, wanda zai rage karfin aiki sosai yayin ayyukan gine-gine, hakan ya haifar da damuwa ga magoya baya da babbar asarar kudaden shiga.

Manchester United, wadda za ta buga Europa League a bana, tana Amurka inda take buga wasannin tunkarar kakar bana.