✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Man City ta doke Atletico Madrid; Liverpool ta lallasa Benfica

An buga wasanni biyu a daren ranar Talata na gasar kofin zakarun turai

Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester City ta yi nasarar doke Athletico Madrid da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin Zakarun Turai.

An fafata wasan a filin wasa na Etihad da ke Ingila, kwallon da dan wasa De Bruyne ya zura jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Wasan dai shi ne zagaye na dab dana kusa da na karshe wato Quarter Final a gasar ta kakar wasannin shekarar 2021/2022.

Atletico Madrid dai na sa ran kai bantenta a zagaye na biyu na wasan da za a doka a gidanta, kamar yadda ta lallasa Juventus a wasanta na karshe a gasar.

Ita kuwa Liverpool, sukuwar salla ta yi har gida a kan Benfica da ci uku da daya a wasan da suka doka a daren ranar Talata.

’Yan wasan Liverpool Konate, Mane da Diaz ne suka jefa mata kwallaye ukun da ya ba ta nasara mafi rinjaye a karawar.