Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester City ta yi nasarar doke Athletico Madrid da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin Zakarun Turai.
An fafata wasan a filin wasa na Etihad da ke Ingila, kwallon da dan wasa De Bruyne ya zura jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
- Harin Kaduna: Tinubu ya ba da tallafin miliyan 50
- DAGA LARABA: Barnar da ’yan bindiga suka yi a Arewa maso Yammacin Najeriya
Wasan dai shi ne zagaye na dab dana kusa da na karshe wato Quarter Final a gasar ta kakar wasannin shekarar 2021/2022.
Atletico Madrid dai na sa ran kai bantenta a zagaye na biyu na wasan da za a doka a gidanta, kamar yadda ta lallasa Juventus a wasanta na karshe a gasar.
Ita kuwa Liverpool, sukuwar salla ta yi har gida a kan Benfica da ci uku da daya a wasan da suka doka a daren ranar Talata.
’Yan wasan Liverpool Konate, Mane da Diaz ne suka jefa mata kwallaye ukun da ya ba ta nasara mafi rinjaye a karawar.