Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haddasa ambaliyar ruwa mai tsanani a wasu sassan ƙasar Saudiyya, lamarin da ya jawo asarar dukiya mai tarin yawa.
A garin Makkah, hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya mamaye hanyoyi, lamarin da ya hana jama’a zirga-zirga.
- ’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra
- Gobara ta yi ajalin ’yar sakataren gwamnatin Sakkwato da ’ya’yanta 3
A wasu wurare, ruwa ya shanye motocin jama’a, wanda hakan ya jefa su cikin mawuyacin hali.
A unguwar Al-Awali, wasu maza sun yi ƙarfin hali domin ceto yaran da suka maƙale sanadin wannan ambaliyar.
Sun haɗa hannu suna taimaka wa juna wajen fitar da yaran daga mawuyacin halin da suka tsinci kansu.
Wannan bai tsaya nan ba, rahotanni sun bayyana cewa wasu a wuraren an gidaje sun rushe, yayin da kayan abinci suka lalace.
A birnin Jeddah, an samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, wanda ya tilasta wa hukumomi dakatar ds zirga-zirgar jiragen sama a wasu filayen jiragen sama.
Domin kare ɗalibai daga lamarin, hukumomin Saudiyya sun rufe ɗaukacin makarantu a ƙasar.
Wannan ba shi ne karon farko da Saudiyya ke fuskanci irin wannan yanayi ba.
A shekarar 2009, birnin Jeddah ya fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani, wanda ya janyo mutuwar mutum sama da 100 tare da lalaga gidaje da tituna.
Har ila yau, a shekarar 2020, wasu wurare a ƙasar sun fuskanci irin wannan matsalar sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
Hukumomin Saudiyya dai na ci gaba da ɗaukar matakai domin rage illar ambaliyar ruwan, ciki har da gina sabbin magudanun ruwa da ƙarfafa tsarin kulawa da muhalli.
Sai dai jama’a na fatan gwamnati za ta ƙara zuba jari a fannin kariya daga irin wannan annoba.