✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mamadou Tandja: Nijar ta yi babban rashi —Buhari

Tsohon shugaban jamhuniyar Nijar Mamadou Tandja ya rasu a ranar Talata yana da shekaru 82 a duniya.

Shugaba Buhari ya bayyana alhinin rasuwar tsohon Shugaban Kasar Jamhuniyar Nijar, Mamadou Tandja wanda rasu yana da shekara 82 a duniya, ranar Talata.

Buhari ya bayyana rasuwar Tandja a matsayin babban rashi a nahiyar Afirka.

Ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar, inda ya ce Nijar ta yi rashin shugaba mai basirar yadda ake tafiyar da siyasa da mulki.

Sannan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Shugaban Jamhuniyar Nijar mai c, Mahamadou Issoufou da al’ummar kasar bisa rashin tsohon shugaban.

Ya kara da cewa Najeriya da ma al’ummarta ba za su taba mantawa da tsohon shugaban nata ba.