Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami ya musanta batun raba motocin alfarma ga Daliget-daliget a Jihar Kebbi, inda ya ce batun shaci fadi ne na magauta.
Yana wannan furucin ne bayan wasu hotuna da suka karade kafofin sada zumunta a kwanan nan na motocin da aka raba ga wasu daga ma’aikatan gidauniyar Khadimiyya, wacce Ministan ya assasa.
Hotunan dai sun janyo kace-na-ce a tsakanin al’umma, har ta kai ga kakakin Malamin, Dokta Umaru Gwandu ya musanta batun.
Shi ma dai Malamin a ganawarsa da ’yan jarida a Birnin Kebbi ranar Talata ya ce batun ya janyo masa suka ta ko ina ba gaira ba dalili.
Ya ce, “Magana ce da ba ta da tushe balle makama, domin kuwa ni ko wani makusancina ba mu ba wa wani daliget abin hawa ba, wasu ne kawai ke son bata mana suna.
“Ina so ku sani cewa wadannan gidauniyoyin biyu wato Khadi Malami da Khadimiyya for Justice and Development Initiative na da zakakuran da suke da kwarewar kawo ci gaba a Jihar.
“Wanda hakan ne ya sa wasu da ke yabawa da aikin na su daga abokansa ne suka siya musu motocin domin nuna jin dadinsu da gudummawar ma’aikatan,” inji Malami.