Wasu limamai da ladanai a Jihar Kano sun ce sun gwammace su daina limanci da kiran Sallah muddin aka tilasta musu yin allurar rigakafin cutar COVID-19.
Malaman sun sanya ayar tambaya kan yadda kasashen da suka ki sayar wa Najeriya makamai ta yaki ta’addanci, suna kuma zargin cewa allurar riga-kafin da za a yi wa shugabanni daban wa wadda za a yi wa talakawa.
- Jini ta hanci ta baki ya rika zuba bayan yi wa wata mata rigakafin Coronavirus a Kaduna
- Miji ya kashe matarsa saboda koko a Neja
- Kotu ta tsare matar da ake zargi da kashe kishiyarta a Neja
- Yau ake rantsar da sabon Shugaban Kasar Nijar, Bazoum
Sun kuma yi bararzanar daina karbar alawus din ga gwamnatin Jihar take ba su, wanda ta ce matukar suna karba to su ne za su zama kan gaba wurin karbar riga-kafin.
Tun bayan da Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje ya ayyana cewa za a fara yi wa limamain jihar riga-kafin cutar, ake ta samun cece-kuce a tsakanin limaman; inda kansu ya rabu biyu, wasu na goyon baya wasu kuma suna nuna rashin amincewa.
Abin da Ganduja ta ce
A jawabin da Gwamnan Jihar ya yi a zaman da ya gudanar da limaman masallatan Juma’a na jihar a kwanakin baya, ya ce in dai har limaman ba su daina karbar alawus daga gwamnati ba, to kuwa dole ne su karbi riga-kafin.
“Babu shakka wannan riga-kafi za a fara ba limamai da na’ibai da ladanai ne, ko ba don komai ba, in dai ba su ce mana sun daina ganin alat ba, to ba za mu manta da su ba.”
Ba mu amince ba —Limamai
Sai dai mafi yawan limaman da Aminiya ta tattauna da su sun nuna rashin amincewarsu a kan riga-kafin.
Malam Lawal Abubakar shi ne Limamin Masallacin Triumph. Ya bayyana cewa ba wai sun ki yarda da allurar ba ce, illa suna neman bayanai a kan ingancinta.
“Abin da muka nema daga gwamnati shi ne a gano inganicn allurar kafin yin ta ga jama’a. Idan kin duba limamai ba allura suke kyama ba, illa suna so a tabbatar da ingancinta kafin a kai ga yi wa al’umma,” inji shi.
Malamin ya kara da cewa, “Mun nuna wa gwamnati shakkunmu game da allurar, musamamn ma muna zargin irin allurar da za a yi wa shugabanni ba ita ce wacce za a yi wa talakawa ba, inda muka ja hankalinsu da su ji tsoron Allah a kan hakan.
“Mun fada musu da su jami’an gwamnati da kuma likitoci da su sani za su tsaya gaban Allah idan har sun san allurar nan ba ta da inganci amma suka kawar da kai don su dadada wa shugabanni, suka bari aka yi wa al’umma to fa za su amsa a gaban Allah.”
A cewarsa, sun shawarci gwamnati da ta kara gudanar da bincike don gano ingancin allurar duba da irin kamfanonin da ke cikin masu samar da rigakafin.
“A kamfanonin da suka yi riga-kafin nan har da Kamfanin Pfizer. Kowa kuma ya san barnar da kamfanin nan ya yi mana a baya, don haka akwai bukatar gwamnati ta sake duba wannan al’amari.”
‘Akwai alamar tambaya’
Malamin ya bayyana mamakinsa game da yadda gwamnati ta mayar da hankali game da riga-kafin, a maimakon mayar da hankali ga harkokin tsaro.
“Abin da zai ba mutum mamaki shi ne su kasashen da ke kawo allurar su ne fa gwamantinmu ta je wajensu don sayen makaman da za a yaki ’yan ta’adda amma kasashen suka ki amincewa su sayar wa Najeriya da makaman.
“Da mutuwar coronavirus da ta rashin tsaro ba duk mutuwa daya ba ce?
‘Gara in bar limanci da ai min allurar’
Shi ma wani limami da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa ba zai taba yarda a yi masa allurar ba, domin a cewarsa, da a yi masa allurar gwamma ya ajiye limancin.
“Wallahi da in yarda a yi min wanann allurar ko kuma in amince a yi wa al’ummar Manzon Allah (SAW), gara a ce na ajiye limancin don ba zan yarda na kai kaina ga halaka ina ji ina gani ba.”
‘Akan N20,000 ake mana gori’
Haka kuma akwai wani hoton bidiyo da Aminiya ta ci karo da shi yana yawo a shafukan sada zumunta, inda wani limami yake bayyana takaicinsa game da gorin da Gwaman ya yi musu akan alawus din da take ba su, inda ya yi barazanar daina karbar kudin matukar aka tilasta musu yin allurer rigakafin.
“Akan alawus din Naira 20,000 ake yi mana gori. To in dai aka ce sai an yi min allurar, to na zabi a daina biya na alawus din. In har sai an juya ni ne to a cire alawus din ba na so.”
Limamin ya ja hankalin gwamnati da sauran al’umma a kan bin dokokin Allah maimakon kame-kame a kan wasu abubuwa daban-daban.
“Abin da ya kamata shi ne a daina barna, a dawo ga tafarkin Allah. Wannan shi ne babban riga-kafi ga kowace irin musiba da za ta tunkaro. Mu tsaya mu yi dogaro ga Allah, wannan shi ne tafarkin tsira a gare mu.”
‘Sai dai in daina kiran Sallah’
Wani ladani da ke ladanci a Masallachin Sheka mai suna Muhammadu Nur, ya bayyana cewa ba zai yarda a yi masa allurar ba.
“Abin da zai faru sai dai a ji shiru babu kiran Sallah, domin ni ba zan yarda a yi min ba ballantana kuma in amince a yi wa iyalina.”
Shi ma wani Na’ibi mai suna Muhammad Chiroma ya nuna rashin amincewarsa game da riga-kafin, inda ya bayyana cewa idan har gwamnati ta matsa, to fa zai ajiye aikinsa.
‘Abin da ya sa na amince da allurar’
Sai dai ga Limamin Masallacin Juma’a na Murtala, Ustaz Kabiru Badamasi Dantaura ya nuna amincewarsa ga yin allurar, inda ya bayyana cewa za su yi biyaya ga umarnin shugabanni, inda ya yi fatan Allah Ya sa hakan ya zama hanyar kakkabe cutar daga cikin al’ummar jihar.
Binciken Aminiya ya gano cewa kusan kaso mai yawa na limaman Kano ba su goyon bayan riga-kafin kuma a shirye suke su bijire wa gwamnati a kan hakan matukar ta hau kujerar na-ki.
Tuna baya
A shekarar 1996, kimanin shekara 25 da suka gabata ke nan, an samu bullar annobar cutar sankarau, inda kamfanin harhada magunguna na kasar Amurka mai suna Pfizer ya ziyarci Jihar Kano da nufin bayar da riga-kafin cutar ta sankarau.
Amma lamarin ya zo da matsala, inda ma aka zargi kamfanin da yin gwajin allurar a kan mutanen Kano.
An yi wa yara sama da 200 riga-kafin a Asibitin Zana a lokacin, inda da dama daga cikin yaran suka rasu, wasu suka samu nakasa kamar kurumcewa ko makancewa, yayin da wadansu da dama suka gamu da larurar tabin hankali.
Tun wancan lokacin da aka samu wannan matsalar, sai mutane Kano da dama suka fara guje wa duk wani abu da aka kawo batun riga-kafi a ciki.
A lokuta da dama, an sha samun labarin inda aka kashe masu yin allurer riga-kafin cutar Polio a Jihar Kano.
Muna goyon shirin yin allurer —Majalisar Limamai
Sheikh Muhammad Nasir Adam shi ne limamin Masallacin Sheikh Ahmad Tijjani da ke Kofar Mata kuma Shugaban Majalisar Limamai ta Jihar Kano.
Ya bayyana wa Aminiya cewa limaman jihar suna goyon bayan shirin na riga-kafin don haka a shirye suke su yi.
Sheikh Nasir ya kara da cewa Musulunci addini ne na wayewa, don haka ba su da ja a cikin duk wani abu da zamani ya zo da shi matukar ba zai taba mutuncin addinin ba.
“Ita rayuwar Musulunci gaba dayanta riga-kafi ce, domin idan kika kalli hukunce-hukuncen tsarki da wanka a Musulunci, duk suna nuni ne a kan riga-kafin kamuwa da cututtuka.”
A cewarsa, sanya su a sahun gaba da gwamnatin ta yi na wadanda za a yi wa riga-kafin, girmamawa ce a gare su, don haka ma a cewarsa ya shirya tsaf don a fara yin allurar ta kansa.
Sheikh Adam ya bayyana cewa gidadanci ne ma a samu mutum ya ki yarda da riga-kafin.
“A Musulunci annoba gaskiya ce, riga-kafi ma gaskiya ne. Don haka gidadanci ne mutum ya nuna rashin amincewarsa.
“Idan za mu iya tunawa riga-kafi aka yi aka kori cututtuka da dama a cikin al’umma, irinsu ’yar rani da kazzuwa da kurkunu da makoko da sauransu.
“Yau ina Foliyo? Ita ma riga-kafi aka yi aka fatattake ta.”
Limamin ya kuma yi kira ga sauran limamai ’yan uwansa da su dauki waccan magana ta gwamna a matsayin raha, duba da cewa shi mutum ne mai raha, ba ya yi ta ba ne da manufar wani abu na gori ga malaman.
Babu dole a batun allurar —Gwamnatin Kano
Aminiya ta tuntubi Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba, inda ya bayyana cewa duk da cewa abu ne mai muhimmanci kowa ya karbi riga-kafin, amma dai babu dole a ciki.
“Babu dole a ciki. Sai dai yana da kyau kowa ya zama ya samu riga-kafin, domin idan mutum ya kamu da cutar kansa ya yi wa.”