Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU) ta zargi Gwamnatin Tarayya da neman gurgunta ilimi da kuma kai malaman makura.
ASUU ta ce jan kafar da gwmanatin ke yi wajen cika alkawuran da suka kulla yarjejeniya wani yunkuri ne gurgunta harkar ilimi da rayuwar matasan Najeriya da ma cigaban kasar.
Kungiyar ta yi zargi gwamnatin na neman kai ta bango saboda yadda ta ke yi wa yarjejeniyar da bangarorin suka kulla dibar karan mahaukaciya.
Abubuwa bakwai muhimmai ne dai gwamnatin ta yi alkawari a yarjejeniyar da bangarorin suka kulla a lokacin da malaman jami’a suka janye yajin aiki.
Abubuwan sun hada da samar da kudade da kuma inganta jami’o’i mallakin gwamnati.
Sauran sun hada da biyan malaman alawus dinsu daban-daban da kuma batun tsarin albashin malaman jami’a da ake takaddama a kai tsakanin bangarorin.
Da yake magana da ’yan jarida, Shugaban ASUU, Reshen Jihar Legas, Kwamred Adelaja Odukoya, ya ce sun dade da fahimtar gwamanti ba ta daukar matakan inganta jami’o’i sai idan kungiyar ta nuna mata jan ido.
A cewarsa batun sabunta yarjejeniyar da suka kulla a 2009 wanda wa’adinsa ya kare a 2012 shi ne mafi dadewa, wanda ya tabbatar da baki biyun gwamnati game da farfado da harkar jami’o’i da cigaban Najeriya.
“Bijirewar gwamnati na sabunta yarjejeniyar 2009 ya jefa malaman jami’a cikin talauci da komawar wasunsu kasashen waje da aiki, gami da lalacewar bangaren ilimin Najeirya,” inji shi.
Game da tsarin albashin malaman jami’a na UTAS da kungiyar ta bullo da shi, Odukoya ya ce gwamnatin ta dage cewa sai dai ta yi musu amfani da tsarinta na IPPIS, wanda kungiyar ke zargin da coge a ciki.
Amma, “Abin da ya fito karara shi she nan gaba UTAS zai ga bayan IPPIS,” kamar yadda ya ce.
Don haka ASUU ta bukaci ’yan Najeriya masu kishi da su shawo kan gwamantin ta cika alkawuran da kungiyar ta kulla yarjejeniya da ita a kansu.
“Idan gwamanti ta ci gaba da nuna halin ko in kula, kungiyarmu ba ta da zabi face ta ci gaba da fafutikar da ta saba,” na yajin aiki domin nuna kishi don ganin an farfado da jami’o’in kasar nan.