✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makudan kudin ayyukan INEC

Hukumar INEC ta kashe jimillar Naira biliyan 122.9 a babban zaben shekarar 2015.

Makonni biyu da suka gabata ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gabatar da kasafin Naira biliyan 305 don gudanar da zaben 2023 ga Majalisar Dokoki ta Kasar.

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya gabatar da kasafin ga Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa a wani bangare na tattaunawa don amincewa da kasafin kudin badi da majalisar ta yi.

Shugaban na INEC ya ce, kasafin Naira biliyan 305 don shirin gudanar da zabubbuka masu zuwa daban yake da na Naira biliyan 40 na tafiyar da ayyukan hukumar.

Da yake bayanin dalilin kasafin kudin, Shugaban na INEC ya ce, an dora wa hukumar nauyin yin zabubbukan cike-gurbi guda takwas – na mazabun tarayya uku na mazabun jihohi biyar.

A cewar Shugaban INEC, “Akwai ayyukan da za a kammala. Muna bukatar canja wasu muhimman kayayyaki kamar akwatunan zabe da kananan rumfunan kada kuri’a da dole a yi su kafin zabe.

“Kuma tilas a kammala zabubbukan fid-da-gwani na jam’iyyu, a mika da sunayen ’yan takara sannan a kammala rajistar masu kada kuri’a kafin zaben.

“Sai buga katin zabe na dindindin da sayo wasu muhimman na’urorin zabe kafin a yi zaben.” Shugaban INEC ya ci gaba da cewa, Naira biliyan 100 da aka riga aka bayar kari a kan kasafin Naira biliyan 40 na shekara ba za su iya yin wadannan ayyuka ba.

Don haka ya bukaci majalisar ta sako sauran Naira biliyan 205 domin ba hukumar damar gudanar da wadannan ayyuka.

Mun damu sosai da yadda zabe a Najeriya ke lakume makudan kudi.

A shekarar 2015, INEC ta yi kasafin Naira biliyan 108 don gudanar da zaben, sai ya tashi zuwa Naira biliyan 189 a zaben 2019.

Hukumar INEC ta kashe jimillar Naira biliyan 122.9 a babban zaben shekarar 2015 wanda idan aka kara wadannan kudade a kan Naira biliyan 305 da INEC ke nema a zaben 2023 da kuma kasafin kudin shekara na Naira biliyan 40, hakan na nufin a cikin shekara 10, INEC ta kashe makudan kudi har Naira tiriliyan 1.124 wajen gudanar da zabe da gudanar da ita.

Haka kuma, idan muka yi la’akari da cewa, Hukumar INEC na samun karin kudade da sauran nau’o’in taimakon fasaha daga cibiyoyin kasashen duniya masu ba da taimako, kamar Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da ta himmatu wajen tallafa mata har zuwa shekarar 2027, ’yan Najeriya suna da hujjar yin tambaya game da wannan kashe makudan kudai da hukumar zabe ta yi.

Akwai dalilai da yawa na yin wannan shakku.

Na farko, duk kudaden da aka kashe suna da dalilinsu, wato, ana iya samun madadin da wannan adadi zai iya samarwa. Ga Najeriya, wadannan kudaden sun yi yawa.

Misali, kudaden da INEC ta kashe a shekara 10 da suka gabata, daidai suke da kudaden da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce, za su iya mayar da daukacin jami’o’inmu na tarayya da na jihohi na gania-fada irin na kasashen duniya a wannan lokaci.

Haka Gwamnatin Tarayya za ta iya amfani da wannan Naira biliyan 305 (da INEC ta nema a kasafin baya-bayan nan), wajen gagarumin rage hauhawar farashin kayan abinci da ake ci gaba da yi da samar da abinci mai sauki ga miliyoyin iyalai na Najeriya da suke ta fama da tsadar kayan abinci.

Ba muna cewa dukkansu daya ba ne, amma a matsayinmu na kasa mai tasowa, kowace Naira da gwamnati ta kashe dole ne a yi la’akari da sauran bukatu masu muhimmanci.

Kuma bayan kudaden da ake kashewa, dole ne a auna kudaden da INEC ta kashe a kan sakamakon zabe.

Gaskiya ce ingancin zabubbukanmu da sahihancin zabe sun samu ci gaba sosai a daidai wannan lokaci da ake nazari, kuma ita kanta INEC ta kara samun yarda da amincewar ’yan Najeriya, kamar yadda aka nuna a muhawarar da aka yi a kwanan baya game da batun zaben.

Hukumar INEC a yau na iya zama cibiyar da ta fi inganci a Najeriya cikin sama da shekara goma da suka gabata.

Kalubalen da aka dade ana fama da su a wasu na’urori da INEC ta sayo tare da tura su wajen yin zabe na bar baya da kura.

Kuma duk da makudan kudin da aka ce an kashe wajen rajistar masu zabe, ilimantar da masu kada kuri’a da wayar da kansu da INEC ta yi, fitowar masu kada kuri’a a zabubbukan ba ta da yawa idan aka kwatanta da na kasashen Afirka da ke da karancin kasafin kudin zaben.

Misalin baya-bayan nan shi ne kasar Gambiya inda yawan masu kada kuri’a a zabe ya kai kashi 90 cikin 100 alhali kasafin kudinsu bai yi ko kusa da namu ba.

Yayin da muka fahimci rawar da INEC ke takawa a dimokuradiyya, bai kamata wannan ya zamo wani shiri na kashe kudade sakaka ba.

Dole hukumar ta sake duba tsarinta na cikin gida don cire kudaden da ba su da muhimmanci da na maimaita ayyuka.

Ba dole ne INEC ta biya kudaden da ake samu daga sauran hukumomin gwamnati da ake amfani da su wajen zabe ba.

Dole ne kuma ta yi taka-tsantsan wajen sayen kayan da suke da inganci don tabbatar da cewa kayan aikin da aka sayo suna da kyau kuma sun dace da fasahar da ake bukata.

Dole ne kuma gwamnati ta tabbatar da cikakken nazari kan yadda INEC ke gudanar da zabe kafin amincewa da duk wani kasafin kudi.

Dole ne mu kula da yadda za a kashe kudaden gudanar da zabe.