A cikin mako guda ’yan ta’adda da ’yan bindiga sun sun rikita lissafin hukumomin tsaro na kasar nan inda suka kai wasu manyan hare-hare tare da sace mutane masu yawa a yankunan Arewa.
A safiyar ranar Alhamis din makon jiya ne ’yan bindiga suka sace tare da yi garkuwa da ɗaliban firamare da sakandare su 287 bayan sace su a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Hakan ya zo ne kwana biyu bayan ’yan Boko Haram sun sace mata 200 a wani sansanin ’yan gudun hijira a Jihar Borno.
- Gwamnatin Nijar ta yanke hulɗar soji da Amurka
- An shiga farautar ɓata-garin da suka kashe sojoji 16 a Delta
Wani malamin makarantar mai suna Sani Abdullahi wanda ya tsallake rijiya da baya ya ce ɗalibai 287 ne aka sace a makarantar.
Malamin ya ce ’yan bindigar sun kashe mutum daya sannan yaran da lamarin ya rusta da su shekarunsu sun kama ne daga takwas zuwa 15.
Sani Abdullahi ya ce, “A bangaren sakandare ɗalibai 187 ne suka bace a bangaren firamare ɗalibai 125 da farko suka bace, amma daga baya 25 sun dawo.”
Malamin ya ce “Na shiga makaranta misalin karfe 7:45 sai na shige ofishin Firansifal, ina ciki sai ya ce min in waiga baya, ina juyawa sai na ga ’yan bindiga sun kewaye makarantar.
“Saboda haka muka ruɗe muka rasa inda za mu shiga. Sai ’yan bindigar suka ce mu shiga daji, kuma muka yi musu biyayya domin suna da yawa kuma ɗaliban kusan 700, suna biye da mu.
“Don haka, lokacin da muka shiga daji, na yi sa’a na tsere tare da wasu da yawa. “Na koma ƙauyen na ba da labarin abin da ya faru.
“Nan take ’yan banga da jami’an tsaro na KADBIS suka bi ’yan ta’addar, amma ba su yi nasara ba, hasali ma ’yan bindigar sun kashe daya daga cikin ’yan bangar,” in ji shi.
Gwamna Uba Sani ya ziyarci makarantar
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sha alwashin kubutar da daliban inda ta yi alkawarin za ta gina ofishin ’yan sanda a garin a yunkurinta na kare rayukar al’umma.
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci makarantar. Ya ce ba zai huta ba har sai an kubutar da yaran gaba dayansu.
Idan ba a manta ba, a watan Janairu wasu ’yan bindiga sun shiga ƙauyen na Kuriga inda suka kashe shugaban makaranta tare da sace matarsa.
Gwamna Uba Sani ya ce dalibai 28 daga cikin fiye da 280 da aka sace sun kubuta daga hannun maharan.
Gwamnan ya ce samar da ’yan sandan jihohi ne zai magance matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.
An tura sojoji Kuriga
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu kuma ya ba da umarnin a tura sojoji domin ceto daliban na Kuriga.
Sace mata ’yan gudun hijira sama da 200
A Borno Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da rahoton Aminiya kan sace mata ’yan gudun hijira kimanin 200 a Jihar Borno.
Majalisar ta soki sace ’yan gudun hijirar, wadanda yawancinsu mata ne wanda aka yi a Karamar Hukumar Ngala ta jihar.
Da yake tabbatar da cewa adadin ya haura 200, jami’i mai kula da harkokin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, Mohamed Malick Fall, ya jajanta wa iyalai da dangin wadanda aka sace, musamman kananan yara, mata da tsofaffi.
Ya ce, “Ina kira ga wadanda suka sace su da su gaggauta sakin su ba tare da wani lahani ba.
“A madadin Majalisar Dinkin Duniya, ina tunatar da wadanda suke wannan mummunan aiki su kiyaye, su bari.”
“Bugu da kari, ina kira ga hukumomi da sauran abokan hulda su dubi yanayin rayuwar ’yan gudun hijira da suke sansanoni a jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya,” in ji shi.
Jami’in ya ce “A halin da ake ciki fiye da mutum miliyan biyu daga jihohin Borno, Adamawa da Yobe ne suke gudun hijira a makwabtan jihohinsu.”
Sace ’yan gudun hijirar da aka yi ya zo ne kwanaki kadan bayan Gwamnatin Jihar Borno ta ce sama da kashi 95 cikin 100 na ainihin masu akidar Boko Haram, musamman wadanda aka kafa kungiyar da su sun mutu ko sun mika wuya.
Mai bai wa Gwamnan Jihar Shawara kan Harkokin Tsaro, Birgediya Janar Ishak Abdullahi (mai ritaya) ne ya bayyana haka a wata hira da Aminiya a Maiduguri.
Ya ce yana kyautata zaton yawancin wadanda aka faro kungiyar da su duk sun mutu, wadanda ke raye a cikinsu ba za su wuce mutum 10 ba.
Abdullahi ya ce, galibin manyan kwamandojin sun mutu ne sakamakon rikicin shugabanci da ya barke tsakanin ’ya’yan Kungiyar ISWAP da ta Boko Haram masu biyayya ga marigayi Abubakar Shekau, bayan ya rasu a shekarar 2021.
Sace almajirai a Sakkwato
A Jihar Sakkwato kuma, ’yan bindiga sun sace almajirai 15 a wata Tsangaya a ƙauyen Gidan Bakuso da ke Karamar Hukumar Gada ta jihar.
Rahotanni sun ce maharan sun sace almajiran ne da misalin ƙarfe 1:10 na dare wayewar garin Asabar.
Shugaban makarantar, Liman Abubakar, ya ce an nemi ɗalibai 15 an rasa, sai dai ya ce ba su tabbatar da adadin ɗaliban da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su ba.
Liman Abubakar ya kara da cewa, wannan ba shi ne karon farko da ’yan bindiga suka kai hari ƙauyen ba, amma ba a taba sace almajiransu ba sai yanzu.
Wakilinmu ya samu labarin cewa, ’yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutum uku a ƙauyen Turba da ke Karamar Hukumar Isa, ciki har da dagacin kauyen.
A wani labadin daban, mayakan Boko Haram sun kona sababbin gidajen da aka gina domin sake tsugunar da ’yan gudun hijira a Karamar Hukumar Dikwa da ke Jihar Borno.
Maharan sun kusta kauyen Gajibo da ke karamar hukumar suna harbi kan mai uwa da wabi sannan suka cinna wa sababbin gidaje 25 wuta.
Kafin nan maharan kungiyar sun yi garkuwa da mutum 101 — kananan yara mata 53 da samari 48 — da suka je neman itacen girki a kauyen Ngala.
Wani ganau, Modu Kundiri, wanda ke hanyar zuwa Maiduguri daga Gomboru, ya ce sojoji sun dakatar da motocinsu na kusan awa wuku a kauyen Logomani kafin daga bisani su bude hanya.
“Na ga akalla 25 daga cikin sababbin gidajen suna ci da wuta a kauyen Gajibo da ke yankin Dikwa,” in ji Modu.
Wani mazaunin garin Dikwa, Sheriff Lawan, wanda ya tabbatar da harin na safiyar ranar Talatar makon jiya da kona gidajen, ya ce maharan sun dasa abubuwan fashewa a wurin da ake aikin ginin gidajen.
Har wa yau ’yan bindiga sun sake kai hari a kauyen Budah da ke Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna a ranar Litinin da dare inda suka sace mutum 30.
Kokarin da Aminiya ta yi don jin ta Kakakin ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mansir Hasan kan hare-haren ya ci tura.