Shugaban Kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya kamu da cutar COVID-19 mako biyu bayan ziyarar da ya kawo Abuja, babban birnin Najeriya.
A ranar daya ga watan Disamba ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Shugaba Ramaphosa yayin taron dangantakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 10.
- Ba a Najeriya ne kawai ake fuskantar kashe-kashe ba – Fadar Shugaban Kasa
- ’Yan bindiga sun kai hari kasuwar Taraba, sun yi awon gaba da mutum 3
Ya kawo ziyarar ne a ranar da Najeriya ta tabbatar da mutum na farko da ya kamu da samfurin Omicron na cutar a karon farko.
A cewar wata sanarwa da Fadar Shugaban Kasar ta fitar, Shugaba Ramaphosa ya kammala ziyararsa a Yammacin Afirka ne kwana biyar da suka wuce.
Sanarwar ta ce sakamakon gwajin da aka yi wa Shugaban da dukkan ’yan tawagarsa ya nuna cewa ba sa dauke da cutar lokacin da suka koma kasar.
Kodayake an yi masa rigakafin COVID-19, Ramaphosa ya fara nuna alamun rashin lafiya bayan ya halarci wani taron tunawa da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, F. W. de Klerk a birnin Cape Town.
Yanzu dai Shugaban na can alamomin cutar sun bayyana a tare da shi, kuma yana samun kulawa.
Shugaban, wanda zai kasance a killace, tuni ya mika harkokin gudanar da mulkin kasar ga Mataimakinsa, David Mabuza har zuwa nan da mako mai zuwa.