Wata babbar kotun lardi dake zamanta a yankin Zuba na Babban Birnin Tarayya Abuja ta aike da wani makiyayi mai suna Umar Shu’aibu zuwa daurin watanni shida a gidan yari bisa kyale shanunsa su yi ta gararanba a filin jirgin sama na Abuja.
‘Yan sanda dai tun da farko sun zargi Umar wanda mazaunin kauyen Bassa na Abujan da keta dokokin iyakar filin jirgin saman.
Dagan an ne alkalin kotun, Alhaji Gambo Garba ya aike da shi gidan kason bayan ya amsa laifin nasa tare da rokar kotun kan ta yi masa afuwa.
Sai dai alkalin ya ba makiyayin zabin biyan tarar N30,000, yana mai cewa kotun ta amince da hakan ne kasancewar ba a taba samunsa da aikata wani laifi ba a baya.
Ya kuma shawarce shi da ya kasance mai kiyaye doka kuma ya zama dan kasa na gari a nan gaba.
Tun da farko dai dan sanda mai shigar da kara, Mista Chinedu Ogada ya shaidawa kotun cewa jami’an tsaron filin jirgin ne suka kama mutumin kafin daga bisani su damka shi ga ‘yan sanda a ranar bakwai ga watan Oktoba.
Chinedu ya ce a ranar da abin ya faru da misalin karfe biyar na yamma, makiyayin ya keta filin jirgin saman na Nnamdi Azikiwe da dabbobinsa da gangan.
Ya ce hakan laifi ne da ya saba da tanade-tanaden sashe na 473 na kundin dokokin Penal Code.