Abin mamaki ba ya karewa a duniya domin a ranar Laraba da ta gabata ne wani makiyayi a Arewacin Indiya ya taune kan wani maciji da ya sare shi da nufin ramuwa.
Kamar yadda kafofiin yada labarai na kasar Indiya suka ruwaito, lamarin ya auku ne a Jihar Uttar Pradesh a lardin Hardoni, inda aka kai mutumin mai suna Sonelal asibiti bayan wasu mutane sun gan shi a sume.
Daga baya mutumin ya shaida wa ‘yan kauyen cewa yana kiwon dabbobinsa a wani fili ne lokacin da macijin ya sare shi. Wanda hakan ya sa ya harzuka ya kama macijin ya taune kansa sannan ya tofar.
“macijin ne ya sare ni, sai na kama shi na taune masa kai baki daya har ya mutu sannan na shigo da shi cikin gari.”
Likitan da ke duba mutumin mai suna Sanjay Kumar ya ce ya yi mamakin yadda mutumin ya rayu bayan ya tauna kan macijin da ke da dafi mai guba.
“ban taba ganin irin wannan ba a rayuwata. Mutumin na nan lafiya duk da cewa ya tauna kan macijin,” inji likitan.
Wadanda suka shaida lokacin da mutumin ke tauna kan macijin sun ce sun yi tunanin ko mutumin ya sha kwaya ne.