✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makiyaya sun kona gidaje 146, mutane 1,600 sun tsere a kauyukan Yobe

An kashe mutum daya tare da kona gidaje akalla 146 rikicin Fulani da makiyaya a kauyukan Gurjiyaje da Maluri

An kashe mutum da daya tare da kona gidaje akalla 146 a wani harin daukar fansa da Fulani makiyaya suka kai wa manoma a kauyukan Gurjiyaje da Maluri a Karamar Hukumar Fika ta Jihar Yobe.

Akalla mutane 1,600 tserewa daga gidajensu sakamakon harin da aka kai kan al’ummar Dogon Kuka da ke zaune a Gurjaje a cikin dare a kauyukan Gurjiyaje da Maluri da ke karamar hukumar.

Hajiya Halima Kyari Joda, kakakin kantoman karamar hukumar, Abubakar Ayuba Idris, ta shaida mana ta waya cewa an kona gidaje 146, mutane 1,686 ciki har da kananan yara, suka yi gudun hijira, zuwa yanukunan Maluri, Garin Ari, Dibbol, Bulaburin da kuma Fika.

Sakamakon haka ne suka kai ziyarar gani da ido tare da Sarkin Fika, Alhaji Muhammad Ibn Abali Idrissa, da dan majalisar jihar da ke wakiltar yankin, Alhaji Yakubu Suleiman Maluri, inda suka jajanta wa al’ummar Gurjaje.

Shaidu sun ce makiyayan sun afka wa al’ummar ne a kan babura inda akasarinsu ke dauke da baka da kibau cikin  jerin gwano.

Rahotanni daga yankunan sun bayyana cewa, makiyayan sun kai farmaki kan mutanen ne bayan wani rikici kan gonakin kankana da shanun makiyaya suka shiga.

Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkareem, ya samo asali ne tsakanin makiyaya da al’ummar manoma a Dogon Kuka a watan Satumba, 2023.

Wata majiya ta ce rikicin farko tsakanin makiyaya da manoma ya faru ne a lokacin da shanun suka lalata gonakin kankana a yankunan da wannan lamari ya faru.

Majiyar  ta tabbatar da  cewa ’yan banga sun kashe makiyaya biyu kuma makiyayan sun yi zargin an sace wasu shanunsu tare da shan daukar fansa.

A halin da ake ciki dai kwamishinan ’yan sandan jihar Yobe ya tura jami’ansa yankin domin wanzar da zaman lafiya da kuma hana ci gaban rikicin.