Malamin Musuluncin nan na Sakkwato, Malam Bello Yabo, ya ce makirci aka shirya da aka kama shi, amma Allah Ya kubutar da shi.
Malamin ya fadi haka ne yayin da yake jawabi ga mabiyansa a masallacin gidansa.
“Amma ya kamata su sani duk abin da ake yi duniya na yi ba abin da nake tsoro – na zauna gidan yari tsawon shekara biyar, na yi asarar sallar idi 10 a lokacin ina tsare kuma a Sakkwato nake ba wani wuri ba”, in ji shi.
- ‘Yan sanda sun yi awon gaba da Shaikh Bello Yabo
- ’Yan Sanda sun kai samame makarantar Islamiyya sun kwashe dalibai 300 a Kaduna
Ya ci gaba da cewa ba a yi wa iyalansa da wadanda ke karkashinsa adalci ba domin an hana ya kammala biya musu bukatun Sallah alhali an san an tsara ba za a bar shi ya yi ta a cikinsu ba.
“Duk Najeriya ba wanda ya isa ya hana min yin wa’azi domin ita ce hanyar da na zaba.
“Na gode Allah ba a kama ni don na yi sata ko neman matar wani ba, sai don na yi wa’azi kuma ba zan bar wa’azi ba har karshen rayuwata”, in ji Malam Bello Yabo.
Ya kuma yi godiya ga wadanda yace sun taimaka aka bayar da shi beli musamman shugaban Kungiyar Lauyoyi ta jihar Kaduna da Ministan Shari’a da Shaikh Yusuf Sambo Rigachukun da Shaikh Isah Ali Pantami da Malam Murtala Bello Assada, wanda ya nada a matsayin Sarkin Yakin Bello Yabo a jawabin.
Da misalin karfe 1.00 na ranar Litinin malamin ya dawo gida, kuma ya samu gagarumar tarba daga magoya bayansa.
A makon jiya ne dai aka ba da rahoton cewa ‘yan sanda sun kama malamin a Sakkwato saboda koken da aka kai cewa ya ci zarafin wasu mutane.
Malamin bai bayyana sunayen wadanda suka yi korafi a kansa ba, sai dai ya ce hukuma ce.