Gwamnatin Jihar Neja ta rufe makarantun sakandaren kwana nan take a Kananan Hukumominta hudu bayan ’yan bindiga sun sace dalibai da malamai daga Kwalejin Kimiyya ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Kagara a Jihar.
Gwamna Sani Bello ya ba da umarnin rufe makarantun ne da safiyar Laraba, sa’o’i kadan bayan an yi garkuwa da daliban da malamansu a makarnatar kwanan da tsakar dare.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da malamai a Neja
- An kama kwamandan Hisbah da matar aure a dakin otel a Kano
Ya ce ’yan bindigar da suka rika bi gidan malamai da dakunan kwanan dalibai sun kashe dalibi daya sannan suka yi garkuwa da mutum 42.
Wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da dalibai 27 da ma’aikata 27 da kuma iyalansu mutum 23.
Kananan Hukumomin da aka rufe makarantun kwanan su ne Rafi da Munya da Mariga da kuma Shiroro, kuma sai abin da hali ya yi.
Gwamnan ya yi kira ga al’umma da su taimaka da duk wani bayani da za su taimaka wajen ceto daliban da sauran wadanda aka yi garkuwa da su.
Adadin wadanda aka sace
Hukumomin makarantar na ci gaba da daukar bayanan wadanda suka rage a makarantar domin tantance adadin wadanda da aka yi garkuwa da su.
Wata majiya ta ce daya daga cikin ma’iakatan makarantar ya samu ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen.
Ta ce wandada aka yi karguwa da su sun hada da Lawal, Ali, Hannatu tare da mijinta, Dodo, da kuma Mohammed Abubakar(Akawu).
Tuni dai jami’an tsaro suka bazama bin sawun ’yan bindigar yayin da jirgin soji ke ta shawagi a sararin samaniya domin gano inda maharan suka yi da daliban da malaman.