Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Bashir Adeniyi Adewali ya ce kimar makamai da miyagun kwayoyi da suka kama a rana guda a Jihar Ribas ya kai Naira biliyan 13.9.
Bashir Adewali ya bayyana cewa makaman biliyan N4.171 suka kama a Tashar Jiragen Ruwa ta Onne da ke Jihar Ribas a ranar Litinin.
Makaman a cewarsa sun hada da bibdigo guda 844 da kuma harsasai masu rai guda 12,500, wadanda aka boye suba cikin kayan daki da aka shigo da su daga kasar Turkiyya.
A tashar jiragen ruwan ne kuma jami’an hukumar kwastam suka kama kwantainoni guda shida dauke da kwalabe miliyan daya na maganin tari mai dauke da sinadarin Kofin.
- Kwastam sun kama makaman N1.6bn a filin jirgin Legas
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Ta-Baci Kan Man Fetur Ke Nufi
Sauran kwayoyin sun hada da kwayar Tramadol guda miliyan 3.5, wanda jimillar kudinsu ya kai Naira biliyan 9.6.
Baya ga su, an kama wasu kwantainoni biyu dauke da kayan gwanjo da kudinsu ya kai miliyan N144.
Shugaban hukumar ya ce mai kayan fasa-kwaurin ya yi yunkurin zille wa bincike domin tantance kayan a tashar jiragen ruwan amma dubunsa ta cika.
Ya ce za a miƙa makaman ga hukumar yaki da kananan makamai da ke karkashin Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, domin gurfanar da mutane uku da aka kama kan zargin alaƙarsu da makaman.