✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majinyata sun koka kan ninka kudin jinya a Asibitin Aminu Kano

Kowa ya san tsadar da man dizal ya yi a kasar nan.

Majinyata da ’yan uwansu suna ci gaba da kokawa game da karin kudin jinya da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) ya yi.

Rahotanni sun ce, a makon jiya ne Asibitin AKTH ya yi karin kudin ayyukan da yake gudanarwa da kashi 100 na abin da ake biya a baya.

Aminiya ta samu rahoton cewa, a baya ana biyan kudin bude fayil a kan Naira 1500, a yanzu kuma ya zama Naira 2,100.

Yayin da a baya ake biyan kudin ganin likita a kan Naira 500, yanzu kuwa ya koma Naira 2000.

Haka kudin da ake biya na tiyatar haihuwar ya tasar wa Naira dubu 120, maimakon Naira dubu 50 da ake biya.

A zantawa da wani magidanci mai suna Umar Amin ya bayyana wa Aminiya cewa, bai san asibitin ya kara kudin ba sai da ya je asibitin.

Ya ce, “Ina zuwa asibitin na AKTH ba tun yau ba. Kuma na san abin da nake biya a baya, amma a wannan lokaci da na zo sai na ji kudin komai ya karu. A gaskiya ban ji dadin hakan ba.

“Ina ganin bai kamata abubuwa su zama haka a asibitin gwamnati ba,” inji shi.

Wata mai juna biyu da ta je awon ciki mai suna Hauwa Mustapha ta bayyana rashin jin dadinta game da karin kudin da ta samu a asibitin.

“Duk haihuwata ta baya a nan asibitin na yi awo, amma wannan karon da na zo na ji kudin ya haura wanda nake biya a baya.

“Don haka, ba zan iya biya ba saboda yanayin da ake ciki,” inji ta.

Wani magidanci da ya kai ’yarsa don duba lafiyarta ya koka game da lamarin, inda ya yi kira ga gwamnati ta kawo dauki don ceton marasa lafiya.

“Wallahi lamarin asibitin nan ya zama wani abu daban. A makon da ya gabaci Sallah na zo asibitin nan kuma na biya kudin da na saba.

“Amma ina zuwa a wannan mako sai na ji an yi karin da ya wuce hankali,” inji shi.

“Talaka da me zai ji, da tsadar abinci ko ta lafiya? Wannan fa shi ne asibitin da talaka yake jin cewa, zai zo ya samu kulawa a kudi kalilan sabanin asibitoci masu zaman kansu, amma sai ga shi asibtin yana so ya zama daidai da asibitoci masu zaman kansu.

“Muna kira ga gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta shiga tsakani,” inji shi.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa, marasa lafiya suna kokawa game da sabon tsarin da asibitin ya fito da shi na biyan kudi ta hanyar Intanet lamarin da ke zama kalubale ga marasa lafiya saboda a lokuta da dama akan samu matsalar rashin ingancin sadarwa (network).

Malam Ado Ali ya ce, akwai lokacin da ya zo zai biya kudi, amma aka samu matsalar netwok lamarin da ya janyo tsaiko wajen duba marar lafiyar da ya kai asibitin a lokacin.

“A lokacin na kai wani danuwana asibiti yana bukatar ganin likita cikin gagagwa, amma sai muka yi rashin sa’a lokacin da za mu biya babu netwok haka muka zauna muna jira har sai da aka samu netwok, sannan muka samu damar ganin likita duk da cewa marar lafiyar na cikin wani yanayi.”

Ya yi kira ga asibitin ya samo wata hanya ta biyan kudi cikin gaggawa don magance wa marasa lafiya wannan matsala.

Hajiya Hauwa Muhammad Abdullahi, ita ce Daraktar Watsa Labarai ta Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ta bayyana wa manema labarai cewa, asibitin ya yi karin kudin ayyukan da yake gudanarwa ne sakamakon tsadar dizal wanda da shi ake amfani wajen gudanar da ayyukan yau da kullum.

“Kowa ya san tsadar da man dizal ya yi a kasar nan. Idan an duba kuma asibitin na da dizal din dai yake gudanar da ayyukansa da suka shafi samar da wutar lantarki da ruwa a cikin asibitin.

“A duk wani asibitin ana kashe miliyoyin Naira wajen sayen dizal,” inji ta.

Hajiya Hauwa ta ce, ya zama wajibi asibitin ya dauki matakin yin amfani da Intanet wajen biyan kudin ayyukansa maimakon biyan kudi a hannu domin toshe hanyoyin cuwacuwa daga ma’aikatan asibitin.