Maganadisun masoyan Mekzikawa
Matattarar masu kaiwa da komowa
Masana’antar warwasawa da watayawa
Hikayar holewa
Tumbatsar tolatsewa
Karfa-karfan karafunan karfafawa
Kundunbalar kadamusawan kundumewa
Kwalam da makwalashen lamushewa
Kwakwar kwacen kwakumewa
Kadandoniyar kudundunewa
Rarrashin rangajin rausayawa
Tangal-tangal din tokarewa
Zugar zagayawa
Zolayar zababbakawa
Zazzabin zogin zaman-tattakewa
Soyayya ce a kwanso
Kowa ya samu kaso
Tunani ne ya taso
Son rai aka kwaso
Annakiyar adawa ke ta naso
Majigin mutsuttsukewa
Masana’antar maganin musgunawa
Damar karamin laujen kayatarwa
Soyewar zukata ba kakkautawa
Masoya na annurin annashuwa
An yi nunin nishadantarwa
Akwakwun hotunan Haurobiyawa
Masu wutsil-wutsil da wuntsilawa
Shirye-shiryen da ake shiryawa
Aika-aika ana dada aikatawa
Manhajar masoya
Maganadisun soyayya
Mirgina-mirginar sanayya
Mahangar kawar da kiyayya
Masalahar lumanar zuciya
Kannen-Audu
Kar ku bi inna rududu
Ku dafa ku hau tudu
Kui biyayya ga Gwaggo Dudu
Mutan Arewaci da na kudu
A bar handama da babakere
Lamarin da ke haifar da sare-sare
A zo ai ta faman gyare-gyare
Gudun kar kasa ta dare
Tuni masu gudu sun rare
Ka ga masu mare-mare
Za su zamto ’yan tabare
Lamura su tabarbare
Mu zamo babu bare
Har magabtanmu su sare
An ce ina batu da yare
Cewa nai rayuka a kare
Ba dawurwurin durwan kare
A kiyayi Harare-harare
Ballantana a kai ga hare-hare
Miyagu su yasar da al’umma su ketare
Dukiya duk sun tattare
Sun haddasa kalare
‘Yan jagaliya sun fandare
Barandami da gariyo an dire
A lura da masu raraka
Zagayowar zabuka
Ayyukan da suka tabuka
Ko sun yi aika-aika
Sai su sa ai ta kiki-kaka
Ga damar karamin lauje
Kar a bari komai ya baje
Managarta a ja mu je
Ban da wasan na jan je
Ai masalaha ciki da waje
Kisan gilla
Babbar kutungwila
Da ake yi wa juna illa
Talaka ya sha bulala
Da balbalin bala’in tsallen tsula
Dama ta sake zagayowa
A baiwa kowa-da-kowa
Ban da dira wawa
Ko asakalar hautsinewa
Wuta a yayyafa mata ruwa
Dunun dugunzumar damuwa
Danniyar hana damawa
Dundumin dulmiyawa
Dalilin durkushewa
Durfafar dambacewar dambarwa
Ai ta kokarin a gyara
A biya diyyar asara
Komai ai karara
Ban da kwado da dara
Sai al’umma ta sarara
Kira shagabannin kabila
Su zamto masu kula
A kiyayi kulla-kulla
Kar zarmewar lamura ta lula
A karke a kila-wa-kala
Bambamin bambance-bambance
Batancin batacce
Batan-baka-tantan
Buruntu da gangan
Baragurbi ya butulce
Batutuwa a tantance
Bilinbituwa a fayyace
Baragurbi ya susuce
Bayani a kai a kaikaice
Babban gari ya fi gaban kwatance
Ina malumma
A hada kai da hukuma
A nusar da mu alama
Sai kowa ya kama
Ai ta ba da himma
Ai kama-kama
Mu kara azama
Kasarmu ta kara kima
Tai dadin zama
Don tabbatar da salama
Wannan ita ce wasika
Kar a ce na rera waka
Hatsin tuwo a kyautata nika
Sana’ar na-duke sai a duka
A bar iska kowa ya shaka
Mai-duka ni na roka
Ya kwance mana sasarin sarka
Mugun zare kar ya zam na saka
Ai maganin kwashi-kwaraf da wadaka
A kawar da sara-sukar wuka
Baban-burin-huriyya
Ka tarairayi Haurobiya
Rayuka a ba su kariya
A alkinta mana dukiya
Tallafin talaka ba shan wuya
Usainin-Babajo
Ka san aikin Baba-ojo
Shagaban masu gwanjo
Ya gwabje su gwarjo
Wajen taka rawar banjo
Gwamna el-Rusau
Ka zama Makasau
Jikan Kwasau
Magabta ka zame musu Korau
Batunka ba ai masa tasau
Mu ci dunun kiyayya
Dubi kasashen da su kai gogayya
’Yan siyasa na hamayya
Amma ba tsiya-tsiya
Kamun hannu ake kowa ya taya
Kundin kadan kudu
Kandamar kunu
Ko kamuwa da kurkunu
Kurda-kurdar hawan tudu
Karambani babu awon mudu
Arewatawa an shiga rudu
Tada kan adda ya yadu
Makirai sun harhadu
Badakalar baudaddu
Daukar alhaki ya sa an kwabdu