Makaransuwa
Wajen Watsattsaken hadin abubuwa
Makarantun ’yan mowa
’Yan lelen uba da uwa
Can ake samun natsuwa
Hasafin haruffa
Kalmomi aka kakkafa
Ana ta kaffa-kaffa
Jimloli an zurfafa
Wai kada a zafafa
Lissafi an lissafa
Hasashen jimmilla an wassafa
Littattafai an wallafa
Alamun ajujuwa rumfa-rumfa
Tsarin nazari an jejjefa
Tsare-tsaren tsirfa
Tsawon gashin tsifa
Tsinin tsiro ya tsattsafa
Tsofai-tsofai da tsufa
Tsarin tsautsayin tsinkayar matsafa
Yanayin karatun ’ya’yan Baffa
Na da kawalniyar siffa
Wani wuri a kikkifa
Sai ka ji ’yan aji sun tafa
Kamar sun ci tuffa
Tuni an kera wasulla
Ba a yin bulala
Sai tarairayar talala
’Yan dugwi-dugwi na walwala
Koyi ka koyar ba wahala
Man kaza ya karya kumallo
Don jin dadin dukan kwallo
Da juyi salo-salo
’Yan wasa an yi abin kallo
Baza bindi da fuka-fukin talo-talo
Bayan goge zufa
An kai wa ilimi caffa
Lafkewar lamfa
Ta sa an bararraje a katifa
Masu tsingaro sun fasa jifa
Gobirawan Yumfa
Jan Gwarzo ya kifa
kura ta lafa
An sa shakwara da jamfa
Wanzan ba ya son jarfa
An dai yi rufa-rufa
Matsalar kan akaifa
Ta zam karfaffa
Ta zame wa al’umma karfen-karfa
A hada hanu a dafa
Makarantun al’umma
Sai an kara himma
Ai ta kama-kama
dalibai ba wurin zama
Wasu a ji suna hamma
kirgar lamba-lamba
kidayar tabarmar kaba
Tarawa da debewa an saba
Raba wa ’ya’yan Abba
Amsar adadi ba tababa
Zubin karatu aka kattaba
Jaddawali aka zuzzuba
Alkaluman sanya dan ba
Na hawa bisa turba
Laifukanmu mu tuba
Majaujawar manhaja
Muna ta ja-in-ja
Na-mujiya kwajaja
Ana ta baje haja
Karatun dankoli baja-baja
Na ga ana muraja’a
A tsakanin ’ya’yan jama’a
A dai koya musu da’a
Don kyautata dabi’a
Cikin kowace sa’a
Akwakwun tuttudo tumbi da tara
kwalam da makwalashe an tara
Taliya ta kawo ziyara
Indon-mami ba ta makara
Ta ciko tumbi tai tabara
Babbaku da farfaru
Na bukatar dabarbaru
Mu koya kar mu kwaru
Lallai mu tattaru
Don kowa ya karu
Kimiyya ta fi gaban kimtsa miya
Tattasai da tumatur na miya
Sinadirai an gauraya
Ma’aunin bincike an juya
Kun yi mata lakabin falsafa
Wasu sun ce kidan dundufa
Ko sarke-sarke aka sargafa
Da masu zaton ta’adar matsafa
Nagoye ne dai ya rarrafa
Adon-gari na tafa-tafa
’Yan dugwi-dugwi na liyafa
’Yan lalle na shakar kirfa
Mahukunta suka kallafa
Mara ta’ido na muskuta wa mahaifa
Maigari ka tallafa
’yan birni a kafa ’yar gwafa
Na karkara ai wa dalibai tufa
Mayafi a yafa
Talakawa mu karfafa
A yau sai an yi da kyau
Ba a samun ilimi zikau
’Ya’ya su sha fura-mai-kyau
Sakanni-in-dire da-kau
Ya kai dan uwa
Tare da ‘yar uwa
Ku zan ki biyawa
dimbin batutuwa
Da ke kaiwa da komowa
Haurobiyawa
Arewatawa
Masu hawan-sa na yawatawa
Takun zamani nake bibiyawa
Lullubin duhu ake tambayawa
Safarar kai kwaya
Shaye-shayen juyin kwanya
Sholin salebar sulmiyawa
Turo-molon solsalewa
Ana ta karafkiyar kwakwariya
Malumma da iyayen Haurobiyawa
Masu Martaba muna dada martabawa
Gamba da gafakar girmamawa
Gangaran mai gangarawa
Alaramman kolon titibiri na ta nawa
Watsatsaken warware wariya
Warwarar waskiya
Walwalin walkiya
Wulwulawar watangaririya
Wa-ka-ci-ka-tashin wafciya
Fara’ar fuskokin furanni
Fafutikar fasko fannoni
Fafatawar fahimtar farin rini
Fululun fullon Fulani
Fataken fatattakar farmakin zamani
Rashewar dirshan ne kashe fatari
Rashin makamar fuka-fukin tashi a gari
Runguma masassabin gudun garari
Ragamar rigimar rigunan fahari
Raka-rakar ribatar gatari
Majaujawa
Juyin juwa-juwa
Manhajar warawa
A makaransuwa aka koyawa
Wainar da anka toyawa
Juhala
An yi mata illa
Adala
Ta kasura falala
Fasalin karatu dalla-dalla
Iyayen dalibai
Sai sun biya matsabbai
Yanzu babu ’yan kwabbai
Daloli da dirhamin Dubai
Musayar Hauro a baibai
Jam’in jama’ar jami’ar Jimrau
Ba a make-maken Makau
Sai da tunanin Tunau
A nesanci mantuwar Mantau
A cimma kasurar kosau