Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya fadi a shekaranjiya Laraba cewa Jihar Kaduna ta ci gaba da kasancewa dankon dinke kabilun Najeriya. Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ziyarar ba-zata a gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, inda ya yaba dabi’ar El-Rufa’i ta rungumar daukacin ’yan Najeriya wajen nada su kwamishinoninsa.
Wadansu jami’an Gwamnatin Jihar Kaduna sun bayyana wa Aminiya cewa ziyarar ta ba-zata ce, domin ba su da masaniya kan zuwansa, kawai ganisa suka yi.
Da yake bayani a lokacin ziyarar, Cif Obasanjo ya ce Gwamna El-Rufai mutum da kasar ke bukata a irin wannan lokaci da ake ciki.
“Najeriya na bukatar mutum irin wannan. Mutumin da akwai yakini a kansa. Duk aikin da aka ba El-Rufai, yana yinsa da kyau,” inji shi,
Cif Obasanjo ya ce mutanen Jihar Kaduna sun yi dacen samun jajirtaccen mutum, sannan ya yaba masa bisa yadda ya zabi mace a matsayin Mataimakiyar Gwamna.
Da yake mayar da jawabi, Gwamna Nasir El-Rufa’i ya bayyana Cif Obasanjo a matsayin abin koyi a gare shi, inda ya ce ya koyi abubuwa da dama da suka shafi mulki a lokacin da ya yi aiki a karkashinsa.