Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta gayyaci Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau, da Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Hussaini Rabiu, don su yi bayani game da wani gangami na jam’iyyar PDP.
Mutane da yawa ne dai suka halarci gangamin don su tarbi Mataimakin Gwamnan ranar Asabar lokacin da ya dawo jihar tun bayan sauya shekar Gwamna Bello Matawalle zuwa jam’iyyar APC ranar 29 ga watan Yuni, 2021.
Shi dai Mahdi Gusau ya ki bin Matawalle zuwa jam’iyyar APC.
Matawalle ya samu tarba daga gwamnonin APC da dama yayin bikin karbarsa da aka yi lokacin da ya sauya shekar.
Majalisar ta bukaci Mataimakin Gwamnan da ya bayyana gabanta ne duba da yadda jihar ke alhinin mutuwar mutane a garin Maradun.
Wata sanarwa da kakakin Majalisar, Mustapha Jafaru Kaura,, ya fitar a daren Laraba ta ce an cimma matsayar gayyatar mutanen biyu ne bayan kudurin da Hon Yusuf Alhassan Kanoma, dan majalisa mai wakiltar mazabar Maru ta Arewa, ya gabatar.
Shugaban Majalisar, Hon Faruk Musa Dosara, ya ce ya gabatar da shawara cewa a aike da goron gayyata zuwa ga Kwamishinan ‘Yan Sanda don shi ma ya bayyana a gaban Majalisar “don yin bayani a kan ko Mataimakin Gwamnan ya samu izini daga wurinsu ko kuma a’a sannan kuma ya bayyana wa Majalisa rawar da hukumomin ‘yan sanda suka taka wajen dakatar da taron”.
Majalisar ta yanke hukunci cewa Gusau da CP Rabiu su bayyana a gabanta a ranar 27 ga watan Yuli, 2021.
Wani na hannun damar Mataimakin Gwamnan ya ce har ya zuwa yanzu bai amsa gayyatar Majalisar ba.