✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dokokin Kaduna ta dakatar Ciyamomi 3 kan zargin almundahana

An zargi shugabannin Kananan hukumomin da almundahanar kudade.

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta dakatar da wasu Shugabannin Kananan Hukumomi uku na Jihar bisa zargin karkatar da wasu kudade.

Kananan Hukumomin da aka dakatar da Shugabannin nasu su ne Kaura da Kagarko da Chikun.

An sanar da dakatarwar ne a ranar Talatar bayan an zargi shugabannin da bayar da kwangiloli ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba.

Kwamitin wucin gadi kan binciken, wanda ’yar majalisa mai wakiltar yankin Lere ta Gabas, Munirat Sulaiman Tanimu, ta jagoranta, ya yi nazari kan harkokin kudin na kananan hukumomi biyar: Chikun, Kaura, Kagarko, Soba, da Birnin Gwari.

Majalisar ta ba da umarnin gudanar da binciken ne bayan wani kuduri da aka cimma a ranar 18 ga Yuli, 2023.

Munirat ta bayyana cewa kwamitin ya gayyaci shugabannin da abin ya shafa domin su samar da takardun kudi da suka hada da bayanan banki daga watan Yuni 2022 zuwa Yuni 2023, asusun ajiya na DVA da aka amince da kasafin kudin na 2022 da 2023 da kuma bayanan kwangilolin da aka bayar da matakan kammala su da dai sauransu.

Bayan nazarin takardun, kwamitin ya gano cewa shugabannin Kaura, Kagarko, da Chikun sun saba wa sashe na 48 na dokar gudanar da kananan hukumomi na shekarar 2018 da sashe na 35 karamin sashe na 25 na dokar gwamnatin jihar Kaduna na 2016.

Ta ce wadannan sassan sun zayyana yadda ya dace da kason kasafin kudi da kuma ka’idojin siyan kayayyakin gwamnatin jihar.

Saboda haka, kwamitin ya ba da shawarar dakatar da shugabannin na tsawon watanni shida masu zuwa kafin kammala bincike.

Haka kuma an umarce su da kada su kasance a sakatarorin kananan hukumomi a wannan lokaci kuma su mika ayyukansu ga mataimakansu

Majalisar ta kuma amince da cewa shugabannin kananan hukumomin Birnin Gwari da Soba ba su taka wata doka ba amma an tsawatar musu kan gazawa wajen kasafin kudin shekarar 2023 da aka amince musu daga ma’aikatar Kananan Hukumomin a kan lokaci.

Da yake tsokaci kan rahoton, kakakin majalisar, Yusuf Liman Dahiru, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya jaddada cewa, ya kamata duk masu rike da mukaman siyasa su guji yin almubazzaranci da dukiyar jama’a.