✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an DSS da na gidan yari sun yi dambe kan sake tsare Emefiele

Bayan hatsaniyar jami'an DSS sun sake tsare Mista Emefiele wanda kotu ta ba da balinsa

Jami’an tsaron farin kaya (DSS) da na hukumar gidajen yari sun ba wa hamata iska a harabar kotu kan wanda a cikinsu zai ci gaba da tsare dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, wanda aka gurfanar a gaban kotun.

Bidiyon lamarin da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jami’an DSS suka ci kwalar wani jami’in hukumar gidajen yari ta kasa, tare da wujijjiga shi a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.

An kwashi ’yan kallon ne a yayin da jami’an ’yan DSS suke kokarin sake kama Emefiele,  bayan kotun ta ba da belinsa a kan Naira miliyan 20 sharadin kawo jami’an gwamnati biyu da suka kai mataki na 16 su tsaya masa, su  kuma damka mata fafso dinsu.

Gwamnatin Tarayya ta gurfanar kan zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, zargin da ya musanta, ya kuma kalubalanci DSS ta kawo hujjojin da ke tabbatar da zargin da take masa.

Bayan bayar da belin nasa ne kotun ta dage sauraren karar har zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba, sannan ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi har sai ya cika sharudan belin.

Bayan dage shari’ar, Emefiele ya ci gaba da zama a cikin kotun saboda gudun DSS ta sake kama shi, a yayin da su kuma jami’an hukumar dauke da makamai suka yi wa harabar kotun cikar kwari, suna jiran fitowarsa.

Sai dai a yayin da wani jami’in gidan yari ya yi kokarin tafiya da shi daga kotun, jami’an DSS suka ki yarda su tafi da shi.

Nan take jami’an na DSS suka umarci ’yan jarida da su fice daga harabar kotun yayin da suke ci gaba da kokarin sake kama Emefiele.

A karshe dai jami’an na DSS sun yi nasarar sake tsare Mista Emefiele, inda suka yi awon gaba da shi a cikin motarsu.