✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta cafke masu shirin daura auren jinsi a Kano

Hisbah ta ce bincike zai ci gaba da gudana yayin da ababen zargin biyu ke tsare.

Hukumar Hisbah ta sanar da cafke wasu mutum biyu da ake zargi da shirin daura auren jinsi daya a Jihar Kano.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa na bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a karshen mako.

Ya bayyana cewa, a cikin wani hoton bidiyo da hukumar ta yi arba da shi, an ga wasu maza biyu — Khalifa da Abubakar — suna sumbatar juna a wurin wani casu da ake zargi an shirya domin murnar baikonsu da aka yi.

Sai dai ya ce mutanen biyu da tuni sun shiga hannu, sun musanta zargin da cewa an shirya casun ne domin murnar zagayowar ranar haihuwar daya daga cikinsu.

A cewar daya daga cikin ababen zargin mai suna Khalifa, ya shirya wa kansa casun ne domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Ya ce a wurin bikin ne wani abokinsa mai suna Abubakar ya sanya masa kek a baki sannan ya biyo da sumbatarsa har baka.

Kwamandan na Hisbah dai ya ce ababen zargin biyu na hannu kuma bincike zai ci gaba da gudana.