Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da hare-haren da dakarun Saudiyya suka kai birnin Saada na Yemen, wanda ya kashe sama da mutum 70.
Mista Guterres dai na so a binciki harin wanda Saudiyya ta kai kan ’yan tawayen Houthi na kasar ta Yemen.
- Ana tafka kazamin fada tsakanin mayakan ISIS da na Kurdawa a Syria
- Matasa na zanga-zanga a Gashuwa bayan soja ya bindige direba
“Babban Magatakardar na kira da a gaggauta gudanar da sahihi kuma adalin bincike kan wadannan hare-haren don a tabbatar da yin adalci,” inji mai magana da yawun Mista Guterres, Stephane Dujarric.
Harin na Saudiyya dai wanda ta kai wani gidan kurkuku, ya hallaka mutane sama da 100 sannan ya jikkata wasu da dama, kamar yadda kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta tabbatar.
’Yan tawayen na Houthi dai da wata kungiyar agaji a Yemen ranar Asabar sun yi ikirarin cewa mutanen da suka mutu yanzu sun haura 82, ko da dai ba a iya tabbatar da hakan ba.
Kazalika, ita ma kungiyar ba da agaji ta Medecins Sans Frontieres, ta ce adadin wadanda aka jikkata a harin kawai ya haura 200.
Ahmed Mahat, jagoran kungiyar a Yemen, ya ce har yanzu akwai gawarwakin mutane a wajen, yayin da wasu da dama kuma ba a san inda suka shiga ba.