✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa ta buƙaci a tura ƙarin sojoji zuwa Borno da Yobe

Majalisar ta bayyana yadda ƙungiyar Boko Haram ke amfani da na’urorin zamani ciki har da jirage marasa matuƙa da kuma ƙarin amfani da abubuwan fashewa.

Majalisar Dattawa ta buƙaci rundunar sojin Nijeriya ta tura ƙarin sojoji da manyan makaman yaƙi zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda na Boko Haram a jihohin.

Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin ƙasar, ciki har da kashe kimanin sojoji goma a garin Marte da ke ƙaramar hukumar Monguno ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, da kuma wani harin da suka kai Gajiram na Ƙaramar Hukumar Nganzai, da sanyin safiyar ranar Talata.

A wani ƙuduri da mai tsawatarwa majalisar, Sanata Tahir Munguno, ya gabatar a ranar Talata, ‘yan majalisar sun ce duk da cewa a baya kashi biyu cikin uku na ƙananan hukumomin Jihar Borno sun kasance ƙarƙashin ikon ‘yan Boko Haram — haɗin kai tsakanin sojoji da ‘yan sa-kai ya taimaka wajen ƙwato ƙananan hukumomin.

Amman zaman lafiyan da aka samu, ya sa hedikwatar yaƙi da ta’addancin ta koma Arewa maso yammacin ƙasar, inda sojin ƙasar ke yaƙi da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Yayin da yake nuna damuwa game da yadda ‘yan ta’addan ke sauya dabarun yaƙin su, Monguno ya bayyana yadda ƙungiyar ke amfani da na’urorin zamani ciki har da jirage marasa matuƙa da kuma ƙarin amfani da abubuwan fashewa da suka ƙera da kansu, lamarin da ya janyo mace-macen fararen hula da sojoji da kuma katse harkokin sufuri.

Majalisar Dattawan, ta yi kira ga shugabannin sojin ƙasar su tura isassun sojoji zuwa arewa maso gabashin ƙasar su kuma tabbatar da cewa an ba su na’urorin zamani domin su daƙile sabuwar barazanar.

Kazalika, majalisar ta nemi kwamitinta kan sojin ƙasa da na sama ya sa ido tare da tabbatar da cewa sojojin sun bi umarnin.