✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa za ta yi wa kasafin 2021 karatu na biyu

Majalisar Wakilai ta kammala karatu na farko a kan daftarin kasafin kudin 2021

Majalisar Wakilai ta kammala karatu na farko a kan daftarin kasafin badi da Shugaban Muhammadu Buhari ya gabatar.

Majalisar ta kuma mika kasafin domin yi masa karatu na biyu a loakcin zamanta na ranar Laraba bayan ’ya’yanta sun kammala tofa albarkacin bakinsu a karatun farkon da aka fara a ranar Talata.

A jawabinsa kafin fara mahawara a kan kasafin, Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya bukaci hukumomin gwamnati su mika wa Majalisar rahoton aiwatar da kasafinsu na wata uku.

Gbajabiamila ya ce hakan zai taimaka wajen sanya hukumomin a mizanin da ya dace yayin nazarin tanade-tanaden kasafin.

Idan ba a manta ba a ranar Alhamis din makon jiya ne Shugaba Buhari ya gabatar da wa Babban Zauren Majalisar Tarayya daftarin kasafin na Naira tiriliyan 13.08.

A dakacin ci gaban rohoton.