Kwamitin Majalsiar Wakilai da ke binciken zargin badakalar kudin man fetur har Dalar Amurka biliyan 2.3 ya yi sammacin Ministar Kudi, Kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed da takwaranta na Shari’a, Abubakar Malami.
Kazalika, kwamitin ya bukaci Sakataren Gwamnatin Tarayya ya bayyana a gabansa a matsayin wani bangare na binciken da yake yi.
Shugaban kwamitin, Mark Tersee Gbillah, ne ya bayar da umarnin a lokacin zaunan da suka yi ranar Talata.
Kwamitin yana bincike ne kan zargin harkallar sayar da danyen mai kimanin ganga miliyan 48 ga kasar China da kudinsa ya kai Dala biliyan biyu da miliyan 400 daga 2014 zuwa yanzu.
Mark ya ce sun aike da sammacin ne da nufin sanin irin rawar da Ma’aikatar Kudin da sauran hukumomin suka taka a zargin badakalar.
Ya ce, “Abin takaici ne cewa Ministan Shari’a da Ministar Kudi duk ba sa nan.
“Abin da muka bukata shi ne su bayyana a gaban kwamitin saboda mun aike musu da bukatar yin hakan a hukimance, kasancewar galibin abin da muke nema a ma’aikatunsu suke.