✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta tabbatar da Chira a matsayin babban mai binciken kudi na tarayya  

Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi bayan wasikar da Shugaba Tinubu ya aike mata.

Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Mista Shaakaa Chira a matsayin babban mai binciken kudi na tarayya.

Har ila yau, ta amince da nadin mutane bakwai a matsayin Kwamishinonin Hukumar Zabe ta Kasa INEC (RECs).

Wadanda aka amince da nadin nasu su ne Etekarnba Umoren (Akwa Ibom), Isah Shaka Ehimeakne (Edo), Oluwatoyin Babalolo (Ekiti), Abubakar Ahmed Ma’aji (Gombe), Shehu Wahab (Kwara), Aminu Kasimi Idris (Nasarawa), da Mohammed Abubakar Sadiq (Neja).

Ragowar ukun sun hada da Anugbum Onuoha daga Ribas, Abubakar Fawa Dambo daga Zamfara da Bunmi Omoseyindemi daga Legas.

An tabbatar da nadin wadanda aka zaba bayan an tantance su a zauren Majalisar Dattawa a ranar Laraba.

A wata wasikar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka karanta a ranar Talata, ta bukaci majalisar ta tabbatar da wadanda ya nada.

A cikin wasikar, Tinubu ya ce bukatarsa ta tabbatar da wadanda ya zaba a majalisar ta yi daidai da tanadin tsarin kundin mulki.

Kwamishinonin da aka tabbatar za su yi wa’adin shekara biyar kowannensu.