Cacar baki kan shirin daukar ma’aikata 774 ,000 aiki na hukumar ayyuka ta NDE ta sa Majalisar Dattakawa korar Karamin Ministan Kwadago da Ingantuwar Aiki Festus Keyamo.
Gwamantin Tarayyar ta yi shirin na SPP ne wanda za a fara a watan Oktoba, da zummar daukar matasa 1,000 daga dukkan Kananan Hukumomin Najeriya 774, da za su yi kananan ayyukan wuci gadi a kan albashin Naira 20,000.
- Buhari ya kaddamar da aikin bututun iskar gas a Arewa
- Majalisar Dattawa ta yi barazanar ba da umarnin kama Lai Mohammed
Majalisar ta gayyaci Keyamo da jami’an NDE, wadda ita ce aikin ke hannunta, domin bin bahasi kan shirin daukar aikin wanda a kansa ne NDE ta kafa kwamitin mutum 20-20 na masu daukar aikin a kowace jiha.
Liki ya fara tashi ne sadda ‘yan majalisar suka yi zargin rashin daidaito a zabar ‘yan kwamitocin, wadanda shugaban NDE Nasiru Ladan ce mutum takwas-takwas daga cikinsu kadai ya san yadda aka zabo su.
Hayaniya ta kaure ne bayan ‘yan majalisar sun bukaci Keyamo ya yi bayani kan bambacin da aka samu a cikin sirri, amma ya ce atafau, sai dai a yi komai a gaban ‘yan jarida don su san yadda aka zabo ‘yan kwamitocin.
Jijiyoyin wuya sun kara tashi ne bayan ‘yan majalisar sun zargi ministan da neman zabar yadda zaman da suka kira zai gunana.
Amma ministan ya kekashe kasa cewa shi bai bai fada musu wata yasasshiyar magana ba.
Su kuma daga nan suka ce masa ya tafi ya ba su wuri.