✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta fara aiki kan kasafin 2021

Majalisar Wakilai ta fara aikin kan kasafin kudin 2021 da Shugaba Buhari ya gabatar

Majalisar Wakilai ta kaddamar da aikin amincewa da kasafin 2021 da Shugaban Muhammadu Buhari ya gabatar.

A zaman Majalisar na ranar Talata ne ta kaddamar da aikin kasafin na shekara mai zuwa bayan kudurin yin hakan da Shugaban Masu Rinjaye, Honorabul Alhassan Ado Doguwa ya gabatar.

A ranar Alhamis ne Shugaba Buhari ya gabatar da wa Babban Zauren Majalisar Dokoki ta Kasa daftarin kasafin na Naira tiriliyan 13.08 na shekarar 2021.

Karin bayani na tafe…