Majalisar Tarayya ta sa baki an dage karin farashin wutar lantarki da zai fara aiki a ranar aiki daga ranar Laraba 1 ga watan Yuli.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ce zaman shugabannin majalisun da Hukumar Kayyade Farashin Lantarki (NERC) da kamfanonin raba wutar (Discos) ya amince a dage karin zuwa farkon shekarar 2021.
- Lawan ya caccaki gwamnati kan cefanar da harkar lantarki
- Kurona: ’Yan kasuwar kayayyakin lantarki sun shiga tasku
“Mun cimma yarjejeniyar dage karin na ranar 1 ga watan Yuli, kuma ni da Shugaban Majalisar Wakilai za mu yi abin da ya dace sannan za mu gana da Shugaban Kasa a kai… karin bai dace a yanzu ba kuma akwai bukatar a yi wasu tanade-tanade tukuna”, inji shi.
Ahmed Lawan ya ce halin da ‘yan Najeriya ke ciki sakamakon matsin da cutar COVID-19 bai dace a yi musu karin farashi ba, domin ko kafin bullar cutar ma ba kasafai suke iya biya yadda ya kamata ba.
Don haka ya ce kafin shekara mai zuwa za su yi aiki tare da kamfanonin wajen ganin sun yi gyare-gyare sun kuma samar da abubuwan da suka dace na samar a wutar yadda ya kamata, kafin a kai ga karin farashin.
Kamfanonin sun yi gaban kansu
A nasa bangaren Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya kalubalanci NERC da kamfanonin kan rashin zurfafa tunani kan irin mummunan tasirin da karin farashin lantarkin zai yi wa ‘yan Najeriya, musamman a halin matsin da suke ciki a yanzu.
Ya kuma caccake su kan yadda har suka cimma matsaya a kan sabon farashin ba tare tuntubar ‘yan Najeriya da majalisa da Shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki ba.
Sai dai gwamnati ta biya cikon
A nasu bangaren, kamfanonin rarraba wutar sun ce, muddin za a dade aiwatar da sabon farashin zuwa sabuwar shekara, to sai dai gwamnati ta dauki nauyin biyan bambancin da ke tsakanin sabon farashin da wanda ake biya a yanzu.