Majalisar Dattawa ta amince a yi wa tsarin mulkin kasar nan garambawul ta yadda dan takarar kai-da-halinka zai iya tsayawa a zabe.
A shekaranjiya Laraba ce majalisar ta amince da wannan kudiri a zaman gyare-gyare ga tsarin mulkin kasar nan da ta gudanar, inda ta sanatocin suka kada kuri’ar da ta amince a yi gyara ga sassa na 65 da 106 da 131 da kuma 177 na Tsarin Mulkin Najeriya domin fadada damar da zabi ga masu kada kuri’a su zabi dan takarar kai-da-halinka a lokacin zabubbuka.
Sai dai Majalisar Dattawan ta yi watsi da bukatar rage karfin Gwamnatin Tarayya da batun kebe wa mata kashi 35 na mukamai inda ta amince da gyare-gyare kan sassa 29.
Majalisar ta kuma yi watsi da yunkurin ceri dokar mallakar kasa daga cikin tsarin mulki da kuma ta kirkiro jihohi da sake fasalin iyakoki bayan shafe awa uku ana kada kuri’a ta hanyar amfani da na’ura.
Daga cikin tanade-tanade 33 da aka tattauna majalisar ta yi watsi da hudu, saboda rashin cika ka’idar biyu bisa uku na sanatoci 73. A lokacin zaman majalisar sanatoci 97 ne suka kada kuri’a daga cikin sanatoci 108, (Anambra ta Tsakiya ba ta da sanata).
Sai dai kuma sanatocin sun amince da gagarumar rinjaye kan a yi gyara ga sassa na 4 da 51 da 67 da 68 da 109 na Tsarin Mulkin. Sassan sun tanadi rigar kariya ga ’yan majalisa tare da tilasta wa Shugaban Kasa ya halarci zaman hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Kasa sau daya a shekara don yin jawabi kan halin da kasa take ciki.
Majalisar ta kuma amince a gyara Rataye na Uku na Tsarin Mulkin don Majalisar Kasa ta hada da tsofaffin shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai.
Majalisar ta kuma kayyade kwana 30 da Shugaban Kasa ko gwamnoni za su mika sunayen wadanda suke so su nada a ministoci ko kwamishinoni da zarar aka rantsar da su.
Sauran gyare-gyaren sun hada da rage shekarun tsayawa takara daga 40 zuwa 35 ga masu son takarar Shugaban Kasa, Gwamna daga shekara 35 zuwa 30, an bar na Sanata kan shekara 35, Majalisar Wakilai da majalisun jihohi daga shekara 30 zuwa 25 domin ba matasa damar tsayawa takara.
Sannan duk wanda aka rantsar a matsayin Shugaban Kasa ko Gwamna don karasa wa’adin zababben Shugaban Kasa ko Gwamna ya tsaya takarar wannan mukami fiye da sau daya.
Sannan sanatocin sun yi gyara wa sashi na 162 na Tsarin Mulkin, inda ta rusa asusun hadin gwiwa a tsakanin jihohi da kananan hukumomi, domin ba kananan hukumomin ’yanci cin gashin kai. Kuma majalisar ta soke hukumomin zabe na jihohi domin kyale Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta rika gudanar da zaben kananan hukumomi a kasar nan da sauran gyare-gyare da dama.
Da yake jawabi bayan kammala gyare-gyaren Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana amincewa da gyaran Tsarin Mulkin da wani cika alkawari.
A jiya Alhamis ne Majalisar Wakilai ta kada nata kuri’ar bayan da aka samu matsalar na’urar a shekaranjiya Laraba.
Wakilinmu ya ce, gazawar wakilan majalisar su fara kada kuri’ar ta faru ne sakamakon rashin gwanancewarsu kan yadda za su yi amfani da na’urar wajen kada kuri’ar, inda suka kwashe awanni suna gwada aiki da ita. A yayin gwajin da ya gudana sau shida na’urar ta rika bayar da sakamako mabambanta kan adadin wadanda suka halarci zaman da kuma sakamakon kuri’ar gwajin. A karshe Shugaban Majalisar Yakubu Dogara ya dage kada kuri’ar zuwa jiya, kuma har zuwa hada wannan rahoto ba mu samu sakamakon zaman ba.