Kwamitin Sake Duba Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na Majalisar Wakilai, ya bayar da shawarar ƙirƙiro sabbin jihohi 31 domin ƙara yawan jihohin ƙasar nan daga 36 zuwa 67.
Shugaban kwamitin, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Benjamin Okezie Kalu ne, ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya jagoranta a ranar Alhamis.
Daga cikin sabbin jihohin da aka bayar da shawarar ƙirƙirar su, akwai Benue Ala, Okun, Okura, Confluence, Apa-Agba, Apa da Abuja, waɗanda za a samar daga jihohin Benuwe da Kogi, tare da babban Birnin Tarayya.
A Arewa Maso Gabas, an bayar da shawarar ƙirƙiro jihohin Amana daga Jihar Adamawa, Katagum daga Bauchi, Savannah daga Borno, da Muri daga Taraba.
A Arewa Maso Yamma, akwai jihohin New Kaduna da Gurara daga Kaduna, Tiga da Ghari daga Kano, da kuma Kainji daga Kebbi.
A Kudu Maso Gabas kuwa, akwai jihohin Etiti, Urashi, Orlu, Aba da Adada, waɗanda za su fito daga yankin gaba ɗaya.
A yankin Kudu Maso Kudu, ana son ƙirƙiro jihohin Ogoja daga Kuros Riba, Warri daga Delta, Bori daga Ribas, da Obolo daga Ribas da Akwa Ibom.
A Kudu Maso Yamma, an tsara sabbin jihohin Toru-Ebe daga Delta, Edo da Ondo, Ibadan daga Oyo, Lagoon daga Legas, Ijebu daga Ogun, Oke-Ogun daga Ogun, Oyo da Osun, da Ife-Ijesha daga Ogun, Oyo da Osun.
Idan wannan shawara ta samu amincewa, Najeriya za ta ƙara yawan jihohinta daga 36 zuwa 67.
Ana kyautata zaton lamarin zai kawo sauyi mafi girma a tsarin gudanarwar Najeriya.