✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maishadda zai angwance da jaruma Hassana

Hassana ta fito a fina-finai da dama, amma ta fi yin fice da fim din Hauwa Kulu.

Fitaccen furodusa a masana’antar Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda zai angwance da budurwarsa jaruma Hassana Muhammad.

Za a yi bikin ne a ranar 13 ga Maris din nan a Masallacin Murtala da ke Jihar Kano.

“Ina farin cikin gayyatar masoya daurin aurena. Wadanda kuma ba za su samu damar zuwa ba, sai a taya mu da addu’a.” Mai Shadda ya rubuta a shafinsa na Instagram hade da katin gayyata a ranar Talata.

Hassana ta fito a fina-finai da dama, amma ta fi yin fice da fim din kamfanin angonta mai suna Hauwa Kulu.

Katin gayyata zuwa daurin auren Maishadda
Hassana wadda Maishadda zai aura

An yi rade-radin Maishadda zai aura wasu mata, inda ko a makon jiya aka ruwaito zai angwance da Aishatu Humaira bayan an yi na auransa da Aisha Aliyu Tsamiya wadda ta amarce a makon jiya.