A ranar Talatar da ta gabata ce Reza Parastesh, dan asalin Iran wanda ya yi kama da dan kwallon FC Barcelona Lionel Messi, ya musanta labarin da ke yawo cewa yana yaudarar ’yan mata, har ma ya yi lalata da ’yan mata 23 saboda tsananin kamarsa da Lionel Messi.
Mai shekara 26 Reza ya ce ya kadu matuka da ya ga yadda labarin ya bazu a duniya musamman a shafin yanar gizo ciki har da shafin sada zumunta na Instagram.
Jaridar Marca ta Spain a makon jiya ta ruwaito cewa ana zargin Reza ya yi amfani da kamar da yake yi da Messi wajen yaudarar ’yan mata 23 kuma ya yi lalata da su.
Sai dai Reza ya musanta labarin a shafin sadarwarsa na Instagram inda ya ce: “Labarin da ake bazawa ina amfani da kamar da muka yi da Lionel Messi wajen yaudarar ’yan mata ina lalata da su, sam ba gaskiya ba ne. Da labarin gaskiya ne da tuni wadansu daga cikin ’yan matan sun tona mini asiri. Wadansu ne kawai ke kokarin bata mini suna, kuma zan yi duk mai yiwuwa in dauki matakin da ya dace.”
Reza Paratesh wanda ya yi kama da Messi yanzu haka yana da magoya baya kimanin dubu 700 a shafin sada zumuntarsa na Instagram saboda sunan da ya yi.
Saboda tsananin kamar da suka yi da Messi ya sa jama’a ke tururuwar daukar hoto ko yin musabaha da shi a duk lokacin da ya shiga bainar jama’a.