Mace biyu da wani jariri sun kubuta daga hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.
- Majiyar Aminiya ta ce ’yan bindigar sun sako iyalan ne bayan mijin matan da ke zuane a kauyen Tsamben-Bakwai ya biya N300,000 kudin fansa.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane a Abuja
- Gobara ta cinye na’urar zaben 5,000 a ofishin INEC
A kwanakin baya ne rahotanni suka nuna mahara sun yi awon gaba da wasu mata biyu cikinsu har da mai danyen jego, ba tare da sun bari ta dauki ko abun rufe jaririn ba.
Wakilinmu ya ce an garzaya da matan da aka sako zuwa asibiti, yayin da mawuyacin halin da mai jegon ke cikin ke karuwa.