✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai gida ya tashi PDP daga sakatariyarta saboda taurin bashin kudin haya

PPD ta bayyana matakin a matsayin yunkurin musguna wa babbar jam’iyyar adawa.

Mamallakin gidan da jam’iyyar PDP take haya a ciki a matsayin sakatariyarta ta Jihar Legas, ya tashe ta daga ciki saboda taurin bashin kudin haya.

Gidan dai na kan titin Adukunle Fajuyi ne a unguwar GRA da ke birnin na Legas.

To sai dai jam’iyyar PDP reshen jihar ta bayyana matakin a matsayin abin takaici saboda ko a kwanan nan, sai da ta biya Naira miliyan takwas daga cikin bashin.

Kakakin jam’iyyar a jihar, Taofik Gani, a cikin wata sanarwa, ya bayyana matakin da mai gidan ya dauka a matsayin abin ban haushi.

A cewarsa, “A iya sanina, na san akwai bukatar mu cika kudin da ake bin mu, a zahirin gaskiya ma, ko a kwanan nan muna shirin biyan wasu, amma ba ni da masaniyar zuwa kotu don a tashe mu.

“Muna fatan wannan ba wani yunkuri ba ne na musguna wa babbar jam’iyyar hamayya a jihar nan ko na tozarta ta.

“Ina da tabbacin an lalata dukkan wasu muhimman takardu ko an dauke su da gangan, don a kawo wa shirye-shiryenmu na 2023 cikas.

“Wannan ba abu ne da za mu lamunta ba, za mu dauki dukkan matakan shari’a da suka dace a kai,” inji sanarwar.