Jami’an tsaro na Amotekun a Jihar Ogun sun kama wani da ake zargin ya shahara wajen yi wa jama’a fashi da abin kunna sigari mai siffar bindiga inda yake jefa tsoro da firgici ga jama’a.
Kakakin Amotekun, kuma Mataimakin Kwamanda Moruf Yusuf ne ya bayyana haka a Abeokuta babban birnin jihar.
Ya ce jami’an kungiyar ne suka kama mutumin mai suna Oluwatosin Ayinde a yankin Agbara da ke birnin.
Ya ce, wanda ake zargin mazunin Unguwar Idanyin ne da ke Agbara a Karamar Hukumar Ado Odo Ota, kuma jami’an sun kama shi ne sakamakon rahoton yunƙurin yi wa wani mai suna Abiodun Ogunbiyi da ke sana’ar acaba fashi da bindigar bogin suna tsaka da tafiya a babur dinsa.
Wanda ake zargi ya fito da bindigar suna cikin tafiya wanda hakan ya sa dan acabar ya faɗi da su saboda tsoro sannan ya kama ihu, hakan ya ja hankalin jami’anmu da ke kusa suka zo wajen.
“Wanda ake zargi ya jefar da jabun bindigar a wata duhuwa kuma bayan an gano ta ya ce da ita yake tsorata jama’a da tilasta musu ba shi hadin kai,” in ji Kakakin.
Daga baya wanda ake zargi Oluwatosin ya amsa laifinsa yayin da ake yi masa tambayoyi ya ce shi dan kungiyar asiri ta Eye Confrontanity ne a jihar.
Jami’an sun miƙa shi ga hannun ’yan sanda don ci-gaba da bincike da kuma daukar mataki na gaba.