Wani direban A-Daidaita-Sahu mai shekaru 22 ya mayar da tsabar kudi Naira miliyan 15 da wani fasinja ya manta a cikin babur dinsa a Kano.
Auwalu Salisu mai shekaru 22 ya mayar wa fasinjan, wanda ya zo Kano yin sayayya daga kasar Chadi kudinsa ne bayan da ya ji ana cigiya a rediyo.
- Wanda ya kashe jaririyarsa mai kwana 1 ya shiga hannu a Kano
- Kabilar da bunsuru ya shekara 15 yana mulki
Naira miliyan 15 din da aka manta sun hada da Naira miliyan 2.9 da kuma miliyan 10.13 na kudin CFA.
Da yake bayani a tashar Arewa Radio, matashin ya ce bai san fasinjan ya yi mantuwar ba sai da ya koma gida zai wanke babur dinsa.
Ya ce, “Da na gaya wa iyayena abin da ya faru sai suka ce in koma in neme su a inda na ajiye su; Daga Badawa na dauke su zuwa Bata, amma na je Bata ban same su ba.
“Sai na koma na ba wa mahaifiyata kudin ta ajiye a kabat dinta. Na matsu in rabu da kudin tunda ba nawa ba ne, kuma ba ni da niyyar taba ko kwabo a ciki domin bai halatta ba,” in ji Auwalu.
Ya ce, shi da iyayen nasa na tunanin matakin da ya kamata su dauka, “Sai na ji cigiya a Arewa Radio, inda aka ba da lambar da za a kira.
“Shi ne na kira mai kudin na gaya masa, ya ce zai zo gidanmu, amma na ce ya bari mu hadu a gidan rediyon, shi ne muka je muka hadu, na ba shi kudinsa.”
Auwalu, wanda ya je gidan rediyon ne tare da mahaifansa, ya ce ba shi da niyyar taba kudin, duk da cewa shi da iyayen nasa na cikin matsin rayuwa.
Mahaifinsa ya ce, “Da kyar muke iya girki sau biyu a yini, ko jiya da kudin ke hannunmu ba mu dora sanwa ba.”
Mai kudin, wanda ya zo Kano sayayya ne daga kasar Chadi ya bayyana cewa har ya debe tsammanin ganin kudin, amma yaron ya dawo masa da su.
Da yake magana ta hannun dan uwansa da ke masa tafinta, saboda ba ya jin Hausa, ya fashe da kuka, inda ya ce bai yi tunanin akwai masu gaskiya irin Auwalu ba.
Ya yi wa iyayen Auwalu godiya bisa kyakkyawar tarbiyyar da suka ba wa dansu, sannan ya yi masa kyautar Naira dubu 400.