✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanda ya kashe jaririyarsa mai kwana 1 ya shiga hannu a Kano

Hisbah a Jihar Kano ta cafke magidancin da ya kashe jaririyar da matarsa haifa saboda ba ya son ’ya mace

An kama wani magidanci da ya kashe jaririyar da matarsa da haifa, mai kwana daya a duniya a Karamar Hukumar Tofa ta Jihar Kano.

Hukumar Hisbah ta jihar ta cafke shi ne bayan wata uku da yin aika-aikan a kauyen Doka da ke Karamar Hukumar Tofa.

Matashin mai shekara 28 ya shaida wa jami’an Hisbah cewa ya kashe jaririyar ce ta hanyar sanya mata fiya-fiya a cikin shayi.

A cewarsa, ya ci burin haihuwar da na miji, “amma sai matata ta haifi mace, shi ne zuciyata ta raya min na kashe yar da aka haifa.

“Bayan haihuwar ne na sayo fiya-fiya na sanya a cikin shayi na ba wa jaririyar ta sha ta mutu,”in ji shi a ofishin Hisbah.

A cewarsa, da farko sai da ya ba wa mai jegon, kwaya ta yi barci domin kada ta ga abin da zai aikata.

“Lokacin da na je sayen fiya-fiyan ne na sayo kwayar barcin da na ba wa uwar ta yi barci, ni kuma ba ba wa jaririyar shayi mai gubar.”

Mataimakin Kwamandan Hisbah mai kula da ayyuka, Mujahid Aminudeen, ya ce za su mika wanda ake zargin ga ’yan sanda domin daukar matakin da ya dace.

Ya ce hukumar Hisbah za ta ci gaba da yin duk abin da ya dace wajen yakar miyagun dabi’u da laifuka, ina ya yi kira ga al’ummma da su kai rahoton duk wanda ba su gamsu da take-takensa ba ga hukuma domin daukar mataki a kan lokaci.